More Podcasts
Wasu ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai da umarnin da Hukumar Kula da Harkar Wutar Lantarki a Najeriya (NERC) ta bai wa kamfanonin rarraba wutar da su biya diyya ga abokan huldarsu da ke rukunin Band A.
NERC ta bai wa kamfanonin wannan umarni ne sakamakon rashin samar wa ’yan Band A ɗin wutar lantarki na aƙalla sa’a 20 a kullum a watan Afrilu.
A cewar waɗanda suke kan rukunin Band B zuwa ƙasa, matsalar wutar ba ta keɓanci ’yan Band A kaɗai ba, galibi ma su suka fi ɗanɗana kuɗarsu saboda rashi wutar.
Ko me ya sa rukunin Band A ne kawai za su amfana da wannan diyya?
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO
- DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai bincika.
Domin sauke shirin, latsa nan