Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a dauke wutar lantarki a ilahirin jihohin yankin Arewa maso Gabas guda shida na tsawon kwana hudu.
A cikin wata wasika da ya aike wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke kula da jihohin shida, TCN ya ce yayin da a wasu jihohin wutar za ta dauke gaba daya, wasu yankunan kuwa karancin wutar za a samu a tsakanin kwanakin.
Jihohin da lamarin zai shafa sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.
- Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000
- DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya
Wasikar wacce ke dauke da sa hannun Jami’in Gudanarwa na Shiyyar Bauchi a TCN, Injiniya J.O Joseph, wacce aka aike wa daya daga cikin kamfanonin lantarkin, ta ce za a dauke wutar ne sakamakon saka babban layin dakon lantarki mai nauyin 330kV a karamar tashar lantarki da ke Bauchi.
Sanarwar ta kuma ce za a yi aikin gyaran ne daga tsakanin 10 zuwa 14 ga watan Yunin 2025.
Ta kara da cewa, “Yadda aikin zai kasance shi ne kamar haka; za a dauke wuta a layin Jos zuwa Gombe a tsawon wannan lokacin domin a samu damar saka manyan turakun dakon lantarki a sabuwar karamar tashar lantarki mai nauyin 330kV da ke Bauchi.
“Hakan na nufin ba za a sami wutar ba a garuruwan Damaturu, Molai, Yola da Jalingo, yayin da tashoshin lantarkin Gombe da Biu za su sami wutarsu ta cibiyar lantarki da ke Dadin Kowa, ita kuma karamar tashar lantarki da ke Baga Road za ta sami wutarta ne daga MEPP,” in ji sanarwar.