✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna so a titsiye El-Rufai kan korar ma’aikata 27,000 a Kaduna — PDP

PDP na ƙara jaddada manufarta ta goyon jagoranci nagari a kowane mataki don ganin an rage wa ma’aikata raɗaɗi.

Jam’iyyar adawa PDP ta buƙaci a gudanar da bincike kan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai dangane da korar ma’aikata 27,000 da ya yi a lokacin da yake riƙe da akalar jagoranci.

PDPn ta miƙa wannan buƙatar ce ga kwamitin da Majalisar Dokokin Kaduna ta kafa domin binciken kashe-kashen kuɗaɗen da gwamnatin El-Rufai ta yi.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren hulɗa da jama’a na jam’iyyar, Abraham Alberah Catoh ya fitar, ta ce, PDP ta yi watsi da abin da ta kira ‘lalata aikin gwamnati’ a Jihar Kaduna.

Catoh ya bayyana haka a yayin bikin Ranar Ma’aikata ta bana, yana mai cewa jam’iyyar PDP a koda yaushe na nuna goyon bayanta ga ma’aikata kan juriya da yadda suke gudanar da ayyukansu a Najeriya baki ɗaya.

“Muna kira ga kwamitin da Majalisar Kaduna ta kafa da zai yi bincike kan El-Rufa’i da ya sake faɗaɗa bincikensa har zuwa kan korar ma’aikata 27,000 da aka yi bisa rashin adalci a faɗin jihar ba tare da an biya su hakkokinsu ba, kuma wannan nuna halin ko in kula ne ga aikin gwamnati,” kamar yadda yake cikin sanarwar.

“PDP na ƙara jaddada manufarta ta goyon jagoranci nagari a kowane mataki a ƙoƙarin da take yi don ganin an rage raɗaɗin da ma’aikata ke fuskanta hatta a ma’aikatu masu zaman kansu wanda shi ne ginshiƙi kuma tubalin bunkasar tattalin arziki.

“Muna kuma taya ɗaukacin ma’aikatan Najeriya murnar zagoyowar Ranar Ma’aikata.”