✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal

Babu takamaiman lokacin dawo da wutar da za a iya shafe sa’o’i kafin kammala gyara.

Miliyoyin mutane sun auka cikin yanayi na duhu sakamakon ɗaukewar wutar lantarki a ƙasar Sifaniya da wasu sassan Portugal.

Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama.

Sai dai asibitoci na gudanar da harkokinsu yadda aka saba saboda suna amfani da injinan janareto.

Shugabar gwamnati a yankin Madrid ta ce “abin da za mu yi shi ne mu nemi gwamnatin tarayya ta ayyana shiri na gaggawa don sojoji su kare doka da oda.”

Kamfanin lantarki na Sifaniya ya ce an gyara matsalar a yankunan arewaci da kudancin ƙasar.

Har yanzu dai ba a san abin da ya janyo matsalar ɗaukewar wutar ba, wadda ta shafi Portugal mai maƙwabtaka.

Bankin Sifaniya ya ce harkokin hada-hada ta intanet na ci gaba da aiki yadda ya kamata, sai dai an ambato wasu masu cirar kuɗi sun fuskanci ƙalubale a na’urar ATM.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafin X, Mai Garin Madrid, Jose Luis Martinez-Almeida, ya buƙaci mazauna da su taƙaita zirga-zirgar saboda fargabar abin ka iya zuwa ya komo.

A Portugal kuwa, masu ruwa sun ce yana iya yankewa nan da kowane lokaci a yayin da jama’a ke tururuwar sayen ababen buƙata a manyan shaguna kamar tocilan, jannarera da batura.

Babban kamfanin lantarki na Portugal, EDP, ya shaida wa kwamstomi cewa babu takamaiman lokacin dawo da wutar da za a iya shafe sa’o’i kafin kammala gyara kamar yadda jaridar Publico ta ruwaito.