An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai.
A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita.
- Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa
- Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu.
Bankin Sifaniya ya ce harkokin hada-hada ta intanet na ci gaba da aiki yadda ya kamata, sai dai an ambato wasu masu cirar kuɗi sun fuskanci ƙalubale a na’urar ATM.
A wani bidiyo da ya wallafa a shafin X, Mai Garin Madrid, Jose Luis Martinez-Almeida, ya buƙaci mazauna da su taƙaita zirga-zirgar saboda fargabar abin ka iya zuwa ya komo.
Sai dai wata sanarwa da hukumar samar da wutar lantarki a Spain ta Red Electrica ta fitar, ta ce da misalin ƙarfe 7 na safiya agogon ƙasar, an samu nasarar dawo da sama da kashi 99 na wutar lantarki a ƙasar.
Haka nan ita ma takwararta ta Portugal ta ce tun cikin daren jiya Litinin, aka dawo da wutar lantarkin da dukkanin tashoshin wutar ƙasar guda 89.
Bayan ɗauke wutar da aka samu a Spain, jami’an ba da agajin gaggawa sun sanar da nasarar kuɓutar da mutane dubu 35 da suka maƙale a jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa.
Har yanzu dai hukumomi ba su bayyana dalilin da ya sa aka samu ɗaukewar wutar lantarkin ba, wanda shi ne karo na biyu da irin wannan mummunar katsewar wutar lantarki ta faru a Turai cikin watanni