✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙarin Albashi: Gwamnati da ’yan ƙwadago sun sa zare

A Jihar Borno akwai ma’aikatan da ake biya albashin Naira 7,000 duk wata.

A ranar Talata da dare ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da yi wa ma’aikatanta ƙarin kashi 25 zuwa 35 na albashinsu; ’yan fansho kuma kashi 20 zuwa 28.

Sanarwar da Mai magana da Yawun Hukumar Kula da Albashi ta Kasa (NSIWC), Emmanuel Njoku ya fitar ta ce ƙarin zai fara aiki ne daga watan Janairun 2024.

Njoku ya kuma shaida wa Aminiya cewa za a biya ma’aikatan cikon ƙarin albashin na watannin da suka gabata.

Kazalika ƙarin albashin da aka yi, yana daga cikin shawarwarin kwamitin mutum 37 daga gwamnati da ’yan kwadago da sauran masu ruwa-da-tsaki da gwamnati ta kafa kan ƙarin albashi, a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Ma’aikata, Bukar Goni Aji, a watan Janairu, duk da cewa Aminiya ta samu rahoton cewa har yanzu kwamitin bai miƙa rahotonsa ba.

Wannan na zuwa ne a daren Ranar Ma’aikata, inda a jawabin Shugaban Kasa na Ranar Ma’aikatan ya jinjina tare da yaba wa ma’aikatan Nijeriya.

A saƙon Shugaba Tinubu, wanda ya fitar ta hannun Kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya ce ba wai kawai albashin ma’aikata ya kamata a inganta ba, har ma da kayan aiki.

Sai dai, Kungiyar NLC ta bakin Mataimakin Sakatarenta, Chris Onyeka, ya ce ƙarin albashin da aka yi bata lokaci ne kawai domin hukumar ba ta da hurumin kayyade mafi karancin albashi na kasa.

“Abin da suka ce sun yi ɓata lokaci ne, ba ya da amfani a wurinmu da wurin ma’aikatan gwamnati,” in ji Onyeka a ganawarsa da wakilimu.

Sai dai duk da cewa wakilinmu ya nemi ƙarin bayani, jami’in na NLC ya ki kara cewa komai a kan lamarin.

Aminiya ta yi kokarin samun karin bayani daga wasu manyan jami’an NLC da takwarorinsu na Kungiyar Manyan Ma’aikata (TUC) amma hakan bai samu ba a daren.

NLC da sauran kungiyoyin kwadago dai na kiran a sanya mafi karancin albashi ya zama wanda zai wadaci ma’aikaci, gwargwadon yanayin tsadar rayuwa a kasar nan.

Sun ce idan za a sa mafi ƙarancin albashi, dole a yi la’akari da yadda farashin kayan masarufi suke tashi, musamman bayan janye tallafin mai da gwamnatin ta yi.

Albashinmu ba ya wuce mako daya — Ma’aikata a Abuja

Aminiya ta ji ta bakin wasu ma’aikata kan yadda suke yi da albashinsu, inda wani ma’aikacin Kotun Lardi da ke Jiwa a Birnin Tarayya, da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce albashin da yake karba a wata ba ya wuce mako guda yake cinyewa.

Ya ce a kuɗin mota kaɗai yana kashe Naira 1,500 wajen zuwa wurin aiki da komawa gida.

Ya ce sauran abubuwan da ke lakume albashin nasa su ne sayen kayan abinci, kuɗin makarantar yara da na gidan haya.

“In takaice maka wahala kawai muke sha, kudin da ake ba mu idan an takura ya kai mana mako, shi ke nan ya kare,” inji shi.

Sai dai ma’aikacin bai bayyana dabarun da yake bi ba wajen samar da kudin da ke kai shi tsawon watan.

Shi ma wani ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da ke zaune a yankin Maraba a tsakanin Abuja da Jihar Nasarawa da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce yana dai aikin ne.

“Kullum ina kashe 1,200 kuɗin mota, sannan ina kashe akalla 1,500 kudin abinci. Ke nan kullum ina kashe 2,700.

“Ka lissafa ka gani, sannan ina da iyali, mata daya da ’ya’ya uku a Kano. Idan ka lissafa, za ka ga kawai muna aikin ne domin da babu gara babu dadi.

“Da zarar wata ya yi nisa, sai dai mu koma cin bashi da ’yar dabaru,” in ji shi.

Wani ma’aikacin mai suna Abdul’aziz ya ce kamfanin gadi da yake yi wa aiki na biyansa Naira dubu 20 ne a wata a matsayin albashin aikin da yake yi a Babban Asibitin Gwamnati da ke Maitama a Abuja.

Ya ce aikin nasa na yini uku-uku ne, sannan a je hutu na kwana uku.

Ya ce, “Sai dai sakamakon tsadar rayuwa na gwammace zama da kwana a wurin aikin na tsawon mako biyu, sannan in ziyarci gida Suleja inda nake haya, inda nake kwana uku kadai a gida.”

Ya ce da wannan kuɗin albashin yake taimaka wa iyalinsa da suka hada da ’ya’ya shida da daukar dawainiyar karatunsu da abincinsu.

Sai dai ma’aikacin ya ce yana hada aikinsa da wanke motocin ma’aikata da na masu ziyarar asibitin a lokacin da yake da sukuni, wanda hakan ke taimaka masa.

“Nakan kuma sayi mudun garin kwaki da yawanci nake ci a matsayin abincina.

“Saboda tsadar abinci a nan zubi na kai Naira 1,200.”

Ya ce kudin mota zuwa garin Suleja daga wurin aikinsa da a baya yake biyan Naira dubu daya, yanzu ya koma Naira 1,200 sakamakon wahalar man fetur da ake fama da shi a yanzu.

Muna rayuwa cikin bashi — Ma’aikatan Kano

Aminiya ta leka rayuwar maaikata don gano yadda suke tafiyar da rayuwarsu da albashin da bai kai Naira dubu 100 ba.

Binciken Aminiya ya gano cewa Gwamnatin Jihar Kano tana biyan wanda ta ɗauka aiki da takardar shaidar digiri Naira dubu 40 zuwa dubu 50.

Malam Sadik malami ne a wata makarantar firamare a Kano wanda yake da mata biyu da ’ya’ya bakwai, ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu yana rayuwar hannu baka-hannu kwarya ne.

“A yanzu sai dai mu ce inna lillahi wa inna ilaihi raji’un domin a yanzu tura ta kai bango.

“Mutum yana aiki amma kamar ba ya yi saboda albashinsa ba ya isarsa gudanar da rayuwa.

“A cikin dan karamin albashina za mu ci abinci, za mu sha, za mu yi wanka da wanki.

“Zan biya kuɗin makarantar yara tare da ba su kudin mota kullum. Ni ma a ciki zan je wurin aiki.

“Idan yara suka yi rashin lafiya a ciki za a saya musu magani. Baya ga wasu bukatun da za su iya tasowa. Ta yaya wannan kudi za su ishe mu?

“Rayuwa ce ta hannu baka hannu kwarya muke yi. A yanzu haka ba ma iya cin abinci sau uku a rana.

“Idan an karya kumallo da safe sai dai da rana a yi ta kame-kamen abin da za a ci. Idan yamma ta yi sai a dora na dare.

“A hakan ma dai albashin ba ya isa. Kafin wata ya kare sai an hada da bashi,” in ji shi.

Wani magidanci mai suna Abdulkadir ya ce halin da ya samu kansa a yanzu ya janyo ya shiga rayuwar bashi.

“Wanann hali da muka samu kanmu a ciki ya sa a kullum a cikin bashi nake wanda ke janyo min fadawa cikin damuwa.

“Domin ni mutum ne da ban ma son karbar bashi.

“A da kafin wannan lokaci ina yin kokari ina tsara albashina har ya kai ni karshen wata ba tare da na ci bashi ba, amma a yanzu al’amura sun sauya saboda tsadar rayuwa albashina ba ya isa, ya zama cewar a yanzu sai na ɗauki bashi idan an yi albashi sai in biya ɗan ragowar kuma kuɗin sai na dan riƙe a hannuna don yau da gobe. A hakan ma wallahi kuɗin ba ya isa,” in ji shi.

Umar Aminu wani ma’aikacin gwamnati ya ce albashinsa ba ya isarsa tafiyar da rayuwarsa ba tare da ya hada da rokon ’yan uwansa taimako ba.

“A yanzu wannan hali da muka samu kanmu a ciki ya janyo sai na hada da neman taimako,” in ji shi.

Shi ma wani magidanci wanda ya yi wa Aminiya bayani cikin tsananin damuwa ya ce batun a ce albashi yana isar ma’aikaci ma bai taso ba.

“A yanzu idan mutum ba wata sana’a ce da shi yake samun wasu kudin ba, to a yi maganar albashi zai ishe shi ko ba zai ishe shi ba bai ma taso ba.

“Domin halin da aka shiga na tsadar rayuwa. Abin da kake iyawa ya fi karfinka a yanzu.

“Abinci sai dai mutum ya ci garau-garau, albashin fa da ya zo ka biya bashi shi ke nan sai dai mutum ya koma ya yi tsugune yana lissafin kwanakin wata don jiran a sake biyan albashi. A kullum a haka rayuwar take, kin ga ai akwai damuwa,” in ji shi.

Malama Lami Usman malama ce a wata makaranta a Jihar Kano ta shaida wa Aminiya cewa tsadar rayuwa ta sa ma’aikata da dama sun zama kananan masu tabin hankali saboda damuwa.

“Wallahi wasu malaman da muke aiki da su sun zama kamar masu tabin hankali. Suna tafiya suna magana.

“Idan kana yi wa mutum magana bai san kana yi ba, ko kuma ku yi magana da mutum an jima kadan sai ya ce ya manta,’’ in ji ta.

Ta ce “Wannan yanayi da aka samu kai a ciki ya janyo ma’aikata da dama sun rame sun fita daga cikin hayyacinsu.

“Akwai wani malami da nake yi masa kallon tsoho ashe ba tsoho ba ne, yanayin da ake ciki ne ya sa shi kama da tsofaffi. Da bakinsa ya faɗa min cewa a 1997 ya kammala firamare.”

Shi ma wani ma’aaikaci da ke aiki a Sakatariyar Audu Bako da ke Kano ya ce tsadar rayuwa ta sa da kafa yake zuwa aiki.

Ya ce, “Ni a yanzu abin da ya fi damuna shi ne tsadar kuɗin mota da nake biya don zuwa wajen aiki, idan har zan biye ta biyan kuɗin mota, to fa duk albashin nawa a kudin mota zai kare.

“Domin a kullum sai na kashe abin da ya kai Naira 700, hakan ya sa a yanzu nake tafiya aiki a kafa.

“Ba zan yi ta wani malami a wurin aikinmu ba wanda a wani wata da kyar ya iya saya wa iyalinsa shinkafa kwano uku. Don Allah kwano uku me zai yi har zuwa karshen wata?”

Dukkan mutanen da Aminiya ta tattauna da su sun nemi gwamnatoci a kowane mataki su taimaka su tsawata wa ’yan kasuwa don ganin sun rage farashin kayayyakinsu ko talaka ya samu saukin rayuwa.

A Jihar Borno akwai ma’aikata masu albashin Naira 7,000

Wasu ma’aikatan gwamnati a Jihar Borno musamman bangaren ilimi a matakin farko wato malaman firamare bisa ga rahoton da Aminiya ta samu yanzu haka akwai malaman da ke karbar albashin da bai wuce Naira 7,000 ba a wata.

A baya gwamnati Jihar Borno ta samu kanta a cikin matsin lamba daga kungiyoyin kwadago inda ta shirya jarrabawar gwajin ga malaman makarantun inda a cewarta, ta yi haka ne gudun kada ta yi kitso da kwarkwata.

Kimanin uku da shirya jarrabawar gwajin ga malaman makarantun firamare a jihar su17,229, malamai 5,400 ne suka samu nasara a jarrabawar, kuma tuni suka fara cin gajiyar sabon albashi mafi karanci na Naira dubu 30.

Aminiya ta tattaunawa da wasu daga cikin malaman makarantun firamare a jihar dangane da wannan lamari.

Malama Talatu malamar makaranta ce a karamar sakandare, ta ce, akalla ta kwashe shekara 14 tana koyarwa amma har zuwa yanzu albashinta bai wuce Naira 7,000 zuwa 8,000 ba, inda ta ce a kullum in za ta wajen aiki sai ta kashe kudin Keke NAPEP kimanin Naira 470.

Wata malamar makarantar firamare da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce a shekarar 2023 ta cika shekara 32 tana koyarwa, amma abin takaici har yanzu albashinta bai wuce Naira dubu 13 ba.

Ta ce a shekarun baya gwamnatin Babagana Zulum ta shirya musu wata jarrabawa wacce ko dan aji biyu a firamare zai iya amsa tambayoyi da aka yi musu, amma aka ce ba su ci jarrabawar ba.

Sai ta ce, “Wannan da me ya yi kama?”

Malamar ta ci gaba da cewa lamarin karancin albashi yana matukar ci musu tuwo a kwarya, domin a rayuwa irin ta yanzu a tarar da malamin makaranta mai iyali amma a ce albashinsa ko Naira dubu 20 bai kai ba, duk da matsin rayuwa da ake ciki a kasar nan.

“Ai ka ga al’amarin na buƙatar sake dubawa daga bangaren Gwamnatin Jihar Borno, alhali akwai ma’aikatan gwamnatin jihar da ba su san da wannan matsala ba domin ana biyansu albashi mai tsoka sabanin na malaman makarantun firamare da albashinsu bai wuce cikin cokali ba kuma ga shi ba mu samun ƙarin albashi na shekara-shekara kana ba a biyan mu kudin hutu da sauransu,” in ji ta.

Shi ma wani malamin makarantar karamar sakandare a Karamar Hukumar Birnin Maiduguri da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa Aminiya cewa “A kullum sukan ɗauka cewa shugabannin jihar ba su ɗauki rayuwar malamin makaranta a komai ba.

“Domin in ba haka ba yaushe za a ce a yanzu akwai malaman da albashinsu bai kai ko Naira dubu 10 ba, ai ka ga abin sai dai mu ce inna lillahi wa inna ilaihin raji’un!”

Don haka malamin ya roƙi Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a matsayinsa na wanda ya san muhimmancin ilimi da malaman makaranta ya kai musu dauki don ganin rayuwarsu ta kyautata kamar kowane ma’aikaci a Jihar Borno.

Aminiya ta samu jin ta bakin Mataimakin Sakataren Kungiyar Malaman Makaranta ta Kasa (NUT), reshen Jihar Borno, Kwamared Bako Lawan a kan ko kungiyar ta san da haka?

Sai ya ce, “Lallai an yi gwaji ga malaman firamare a shekarar 2021 da haɗin gwiwa da Kungiyar NUT da Gwamnatin Jihar Borno, inda a cikin malamai 17,229 malamai 5,400 ne kacal suka ci jarrabawar gwajin kan kwarewar aiki da a yanzu suke cin gajiyar albashi mai tsoka alhali sauran mafiya rinjaye da ba su ci gwajin ba su ne ke samun wannan albashi mai karancin da ake magana a kai.

Ya ce su ɗin ma akwai da yawa daga cikinsu da ke da kokari amma ba su da kwarewa, Gwamnatin Jihar Borno na shirin sake horar da su kan aikin koyarwar,” in ji shi.

Shugaban Hukumar Ilimi Bai-Daya (SUBEB) a Jihar Borno, Farfesa Bulama Kagu da manema labarai ke tambayarsa kan ko yaya matsayin gwamnati a kan wannan korafi cewa, har yanzu akwai malaman da ke karbar albashi kasa da Naira dubu 10 a jihar.

Sai ya amsa da cewa, “Lallai akwai wannan bayani kuma Gwamnatin Borno na kan bakarta a kan hakan har sai sun samu kwararrun malamai.

“Amma duk da haka Gwamnatin Jihar Borno a halin da ake ciki ta shirya tura malaman da ba su da kwarewa zuwa manyan kwalejojin ilimi don horar da malaman in sun kammala za su fito su ci gajiyar albashi mai kyau in Allah Ya so,” in ji shi.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Injiniya Lawan Abba Wakilbe ya ce “Duk wani ƙwararren malami muna biyan sa albashi mai kyau, waɗanda ake biya irin wancan albashi ba ƙwararru ba ne, kamata ya yi a ce mun sallame su.”

Ya ce “Masu takardar NCE, muna biyan su Naira 52,000, Digiri kuma daga Naira 60,000 zuwa sama, waɗanda kuma suka yi nisa muna biyan su 100,000 har sama da haka.