Al’ummar Sakkwato nata ce-ce-ku-ce kan dokar da majalisar dokokin jihar ta yi kan soke kayan lefe da takaita tsadar aure da bukin suna a fadin jihar.
Sabuwar dokar soke lefen an samar da ita ne da nufin saukaka ga bukukuwan aure da radin suna, ganin yadda hidindimun aure suke da wahalar gaske a jiha.
Dokar da ke jiran Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ya sanya mata tana da alaka da wadda aka yi a shekarar 1992, aka sake yi mata gyaran fuska a 1996.
Dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Yabo, Abubakar Shehu Yabo, wanda shi ne ya gabatar da batun gyaran dokar da ta samu amincewa a zauren majalisar, ya ce an yi haka ne da nufin rage almubazaranci a harkar bukukuwa a Jihar Sakkwato.
- HOTUNA: Bikin kaddamar da littafi kan mahaifiyar Sarkin Kano da Sarkin Bichi
- Shugaban karamar hukuma ya rasu ana dab da rantsar da shi a Yobe
Honarabul Shehu Yabo ya yi bayanin cewa majalisa ta aminta da yin dokar ne saboda korafe-korafen da al’ummar jihar suke ta yi kan tsadar hidindimun aure.
Ya ce dokar ta kashe lefe sai dai a yi wa amarya kayan sawa kala 10 da sauran kayan kwalliya don buki kawai.
An kuma tanadi hukuncin daurin wata daya ko biyan tarar Naira dubu 50 ga duk wanda ya saba dokar. Amma dokar Musulmai kadai ta shafa, wadanda ba Musulmi ba a jihar za su yi aurensa yadda yake so.
“Kowa ya sani a yau aure ya zama wani babban kalubale ga matasanmu saboda matsalar tattalin arzikin da yin wasu abubuwa da ba dole ba, kawai don gadara.
“Wadannan bakin al’adu na rashin hankali su ne ke kara kawo rikici a cikin aure har sakin aure ya yawaita a cikin al’umma,” a cewar Shamaki Yabo.
Ya ce sabuwar dokar ta tanadi duk wanda zai kai kayan na-gani-ina-so ko neman damar zance da yarinya, zai kai kwali biyu na alewa da huhun goro biyu da kudin da bai wuce Naira dubu 20 ba, amma sadaki ba a kayyade ba, kamar yadda addini ya shar’anta.
Dalilin tsadar aure a Sakkwato
Jamilu Altine Kware ya bayyana cewa a Sakkwato in dai mutum zai yi aure, to mafi karancin kudin da angon zai kashe shi ne Naira miliyan daya.
“Naira dubu 150 a kayan na-gani-ina-so, dubu 150 kudin sanya amarya a lalle, lefe na dubu 300, akwatin dubu 100 sai ka ba amarya dubu 50 kudin buki.
“A gefen amarya kuma uwayenta na bukatar miliyan daya da dubu 500 domin saya mata kayan daki da gado da kujeri da kayan kicin da na gara da sauransu,” a cewarsa.
Malam Musa Ubandawaki na ganin a Sakkwato duk wanda zai yi aure akalla sai ya kashe milayan daya da dubu 400 kafin a kawo masa amarya.
“Mu a nan biyan sadaki da sauran abubuwan da za a yi za su lakume akalla dubu 350” a cewarsa.
Aminiya ta fahimci hidimar aure na farawa daga lokacin da namiji ya hadu da macen da yake son ya aura kafin ya gabatar da kansa ga iyayenta.
Kayan aure sun hada da kwalayen minti da lemun kwalba da kwalayen biskit da kwandon goro da kudin addu’a, wadanda ake kaiwa gidan wadda ake so tare da rakiyar dangin namiji da abokansa.
A cewar Malam Mustafa Muhammad, kayan da ake farawa da su na-gani-ina-so a yanzu sun hada da katon 10 zuwa 20 na lemun kwalba, gwargwadon karfin dangin da za su kai kayan, sannan a hada da Naira dubu 100 na kyauta da za a bai wa yarinya.
“Da yawan idan ka ga kayan za su isa a bude shagon tireda, su kuma dangin amarya idan za a kai kayan za su shirya abincin alfarma ga dangin namiji da in sun zoza su ci kuma su tafi da shi.
“A satin da ya wuce yayata take fada min ta kashe sama da Naira dubu 100 a wurin dafa abincin masu kawo kayan auren ’yarta,” in ji shi.
Muhammad ya dora laifin tsadar hidimar aure a jihar a kan al’adun da suka haifar da sanya tsammani a tsakanin dangin biyu.
“Idan har dangin amarya suka gaza abin da dangin ango suka yi tsammani, sai ka ga ba su yi murna ba domin lamarin ya koma kwarya ta bi kwarya, wanda yawanci shi ke haifar da matsala har ya shafi auren gaba daya,” in ji shi.
Dokar ta yi daidai
Wani malamin addini a Jihar Sakkwato, Shaikh Habit Sani Maihula, ya ce akwai matukar muhimmanci ga mutane su bi abin da addinin ya tsara a harkar aure, domin addini ya hana almubazaranci a harkar aure.
“Matsalar almubazarancin ne ya shafi kannenmu da suka isa aure sun kasa yi ga su nan zaune cikin al’umma.
“In ka ce mutum dole sai ya kashe miliyoyi kafin ya auri mace, ka ga duk wanda yake son ya yi aure dangi guda sai ya wahala kafin bukatarsa ta biya, Musulunci bai kayyade sadaki ba amma wannan almubazaranci a cikin aure bai aminta da shi ba.
“Tun da har an samar da doka akwai bukatar gwamnatin jiha da Majalisar Sarkin Musulmi da malamai a jiha da sauran masu ruwa da tsaki su samar da hanyoyin hana almubazarancin a cikin aure,” a cewarsa.
Maman Aishat da ke zaune a uguwar Mana ta ce dokar abar farin ciki ce ga dukan iyalai a Jihar Sakkwato, inda ta yaba wa majalisar dokokin kan yi wa dokar gyaran fuksa.
Sadaukin Sakkwato, Malam Lawal Maidoki, ya yaba wa ’yan majalisar sannan ya roki mutanen jihar da su yi wa dokar biyayya bayan an sanya mata hannu.
“Abin da ’yan majalisar suka yi haka Musulunci ya yi tsammanin su yi, wannan dokar kadai na iya sanadin shigarsu Aljanna, abin da ya rage shi ne kan duk wani Musulmi ya bi dokar in gwamnan jiha ya sanya mata hannu ta zama doka,” a cewrsa.
Musulunci bai hana ba
A hirarta da Aminiya, Malama Sa’adatu Haruna Illo ta ce ba ta ga laifi a wannan al’adar ba, domin yabawa da nuna godiya ce a tsakanin masoya.
“Ba na goyon bayan sokewa, yin wadannan kayan ba wani abin damuwa ba ne, kawai abu ne na nuna farin cikinka ga wacce ta amince za ta aure ka,” a cewarta.
Ta kara da cewa yin kayan bai saba wa addini da al’ada ba domin “maganar gaskiya Allah Ya umarce mu da saka abu mai kyau da abu mai kyau.”
Ta ce mutane sun kasa fahimtar yadda lamarin yake ne domin “ba wata doguwar wahala ce ba, alewar Naira 50 ta isa, ba dole sai an sayi kwalaye ba, in dai akwai soyayya.”
Dokar ba za ta yi aiki ba
Wani malamin addini kuma, Shaikh Isa Talatar Mafara, shi kam bai goyi bayan dokar ba, inda ya ce ta ci karo da Musulunci.
“’Yan majalisar dokoki ba su da damar yin dokar kayyade kudin aure saboda shari’a ta zaburar da kowane mutum ya auri daidai da shi, waton kwarya ta bi kwarya.
“In kai ba mai kudi ba ne kar ka je ka auri diyar mai kudi domin ba za ka ji dadin auren ba.
“A lokacin gwamnatin Bafarawa an taba kokarin irin wannan dokar, aka zo neman shawarata na gaya masu ko an yi ta ba za ta yi aiki ba, na ba su misali da Sarkin Musulmi Maccido a lokacin na ce in za ka auri diyarsa kwandon goro biyu zai isa, na tabbata ko kwandon goro 100 ba zai ishe su ba.
“A yanzu mutum zai auri diyar gwamna, kana tsammanin za su karbi dubu 10 kudin addu’a ko kwalin minti biyu?
“A lokacin da nake fada masu matsayata, na gaya masu wannan dokar ba za ta yi aiki ba don masu mulki ne farkon wadanda za su karya ta.
“Dokar za ta shafi talaka ne kawai don ba a iya gudanar da ita ga masu matsayi ko masu kudi a jiha,” a cewarsa.