✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Bikin kaddamar da littafi kan mahaifiyar Sarkin Kano da Sarkin Bichi

Sarkin Musulmi da sauran sarakuna daga Kudu da kuma Arewancin Najeriya tare da sauran manyan baki daga ciki da wajen kasar sun halarci bikin.

A ranar Alhamis ne aka kaddamar da litattafi kan tarihin rayuwar marigayiya Maryam Bayero mahaifiyar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero a Abuja.

An yi kaddamarwar ne a wani kasaitaccen biki, inda Sarkin Musulmi da sauran sarakuna daga Kudu da kuma Arewancin Najeriya suka halarta tare da sauran manyan baki daga ciki da kuma wajen kasar.

Ga yadda bikin ya gudana a cikin hotuna:

’Ya’yan marigayiya Mai Babban Daki — Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da dan uwansa Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero a rike da littafin a wajen bikin (Hoto: Al Amen Umar/Kamal Photos)
Sarkin Musulmi tare da sauran sarakunan da suka halarci bikin kaddamar da littafin. (Hoto:Al Amen Umar/Kamal Photos).
Sarkin Musulmi tare da gwamanan Kano da mataimakinsa da wasu manyan baki a yayin kaddamarwar Hoto: Al Amen Umar/Kamal Photos
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje yana gaisawa da Sarkin Kano a wajen taron (Hoto: Al Amen Umar/Kamal Photos).
Sarikin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero tare da Sarkin Kano Muhammad Sa’ad Abubakar da kuma ‘yar uwan marigayiyar a wajen kaddamarwar. (Hoto: Al Amen Umar/Kamal Photos).
Wasu sarakunan Arewa da na Kudu tare wasu manyan baki a taron (Hoto: Al Amen Umar/Kamal Photos)
Sarkin Kano da Sarkin Bichi tare da wasu makusantan marigayiyar a wajen taron. (Hoto: Al Amen Umar/Kamal Photos).