Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nemi goyon bayan basaraken Filato, wato Gbong Gwom Jos, Jacob Gyang Buba wajen sake gina babbar kasuwar Jos.
Sarkin na Kano ya yi kiran ne a fadar Gwong Gwom na Jos a yayin da kai ziyara ga basaraken a ranar Juma’a.
- HOTUNA: Sarkin Kano ya bude cibiyar kula da masu cutar kansa a Ribas
- ’Yan bindiga sun sace Basarake a Jos
Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya yi dogon jawabi kan dangantakar masauratar Kano da ta Jos, ya kuma jaddda irin muhimmancin kasuwar da kuma kyakkyawar alakar kasuwanci da ke tsakanin Kanawa da Jasawa.
Sannan ya yi kira ga basaraken da kuma masarautar jihar da ta bayar da goyon bayanta ga kokarin sake gina kasuwar da Gwamnatin Jihar ta ke yi da hadin gwiwar wani bankin kasuwanci.
Sarkin na Kano ya kai ziyara fadar basaraken na Jos ne a cikin ziyarar da yake yi a jihar.
Jacob Gyang Buba kuma shi ne shugaban Majalisar Sarakunan jihar Filato.