✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aminu Bayero ya naɗa Sanusi a matsayin Galadiman Kano

A gefe guda kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Mannir Sanusi a matsayin Galadiman Kano.

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero, a matsayin Galadiman Kano, bayan rasuwar Abbas Sanusi.

A gefe guda kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, wanda ke ta ƙaddamar kan sarautar Kano da Aminu Ado Bayero a gaba kotu, ya naɗa Mannir Sanusi a matsayin Galadiman Kano.

Wannan lamari na nuni da cewa rikicin Sarautar Kano ya ɗauki sabon salo, inda kowanne daga cikin ɓangarori biyun ya naɗa nasa Galadiman Kano, inda masu riƙe da sarautun biyu za su gudanar da ayyukansu daban-daban.

A cikin wasiƙar da ke ɗauke da wannan sanarwar, wadda Alhaji Awaisu Abbas Sanusi, babban jami’in gudanarwa na Majalisar Masarautar Kano ya sanya hannu, naɗin Sanusi Ado Bayero ya biyo bayan taron majalisar da Sarki Aminu ya jagoranta a ranar Laraba, 16 ga Afrilu, 2025.

A baya an naɗa Sanusi a matsayin Chiroman Kano, dan Majalisar Masarautar Kano, kuma Hakimin Gwale a zamanin mahaifinsa Sarki Ado Bayero.

Bayan rasuwar mahaifin nasa a shekarar 2014, a matsayinsa na babban ɗa kuma magaji, an ɗauka cewa Sanusi Ado ne  wanda ya cancanci ya gaje shi, War wasu rahotanni na farko sun sanar da shi a matsayin Sarki.

Sai dai, a ranar 8 ga Yuni, 2014, aka naɗa ɗan ɗan uwansa, Sanusi Lamido Sanusi, a matsayin Sarkin Kano. A sakamakon haka, Sanusi Ado ya ƙi yin mubaya’a a gare shi kuma, don nuna rashin amincewa, kuma ya yanke shawarar barin Kano.

Bayan raba Masarautar Kano, da cire Sarki Sanusi II, da kuma naɗin ƙanensa, Aminu Ado Bayero, a matsayin Sarki na 15 a watan Yulin 2020, an mayar da Sanusi Ado Bayero kan matsyinsa a Majalisar Masarautar Kano kuma aka ba shi sarautar Wamban Kano.

Tarihin Sanusi Ado Bayero

Sanusi kammala digirinsana farko a fannin shari’a a shekarar 1983 kuma an rantsar da shi a matsayin lafiya a shekarar 1984.

Tsohon ma’aikacin Gwamnatin Jihar Kano ne inda ya yi aiki daga 1985 zuwa 2015, har ya kai matsayi mafi girma na Babban Sakataren.

Daga baya aka naɗa shi a matsayin Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, muƙamin da ya riƙe har zuwa lokacin da aka cire shi a watan Agustan 2015.