✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A binciko mesar da ta ɓace a Kano — Sanusi II

Ana zargin tsohon Akantan-Janar na kasa da kiwon namun dajin da suka hada da zakuna, da kada, da macizai da kuma mesa.

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga kwamishinan ‘yan sanda Ibrahim Adamu Bakori, da ya tsaurara bincike domin gano mesar da ake zargi mallakin tsohon Akanta-Janar Ahmed Idris ce ta kuɓce kuma ta shiga gari.

Sarkin ya yi jan hankalin ne lokacin da al’ummar unguwar Daneji, bisa jagorancin mai unguwar Malam Abba Lawan suka kai masa koke, kan yadda tsohon Akantan ya ajiye dabbobi masu hadari a gidansa da sunan kiwo, har ake yanka musu shanu domin ciyar da su.

Sarkin ya kuma ja hankalin tsohon Akantan kan illar ajiye dabbobin a tsakiyar jama’a, tare da yin kira a gare shi da ya gaggauta dauke su, domin gudun abinda ka-je-ka-zo.

Idan za a iya tunawa dai Aminiya ta rawaito yadda ake zargin Akantan da kiwon namun dajin da suka hada da zakuna, da kada, da macizai da kuma mesa, har ma yake yanka musu shanu a bainar jama’a.

A tattaunawarmu da Mai Unguwar, Malam Abba, ya bayyana mana yadda ya jagoranci al’ummar har gaban Sarki, domin neman dauki.

“Lamarin ya faru kafin ranar Juma’a, amma ba mu samu tabbas ba har sai ranar Juma’ar. Na je na same shi da kaina na yi masa magana, na kuma fada masa illar ajiye dabbobi masu hadari a tsakiyar al’umma ya kuma yi min alkawarin zai kwashe.

“Da fari ma da cewa ya yi ba yanzu zai kwashe ba, sai na ce masa sai sun yi girman da za su hadiye wani tukunna? Sai ya ce “za a dauke”.

“Da na ga bai kwashe ba, sai na rubuta rahoto na aika wa Wakilin Kudu, shi kuma ya aika wa Wakilin Hakimi, har zuwa gaban Sarki.

“A yau kuma mun je gaban Sarki mun sanar da shi halin da ake ciki. Kuma an karanta masa takardarmu, ya kuma bayar da umarnin mu je a rubuta wa kwamishinan ‘yan sanda a hukumance, domin su ne suke da hakkin binciken abinda yake gudana.

“Muna sa ran gobe Talata za a kai takardar in sha Allah,” in ji shi.