✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kano ya nemi goyon Gbong Gwom Jos wajen sake gina kasuwar Filato

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nemi goyon bayan basaraken Filato, wato Gbong Gwom Jos, Jacob Gyang Buba wajen sake gina babbar kasuwar Jos.…

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nemi goyon bayan basaraken Filato, wato Gbong Gwom Jos, Jacob Gyang Buba wajen sake gina babbar kasuwar Jos.

Sarkin na Kano ya yi kiran ne a fadar Gwong Gwom na Jos a yayin da kai ziyara ga basaraken a ranar Juma’a.

Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya yi dogon jawabi kan dangantakar masauratar Kano da ta Jos, ya kuma jaddda irin muhimmancin kasuwar da kuma kyakkyawar alakar kasuwanci da ke tsakanin Kanawa da Jasawa.

Sannan ya yi kira ga basaraken da kuma masarautar jihar da ta bayar da goyon bayanta ga kokarin sake gina kasuwar da Gwamnatin Jihar ta ke yi da hadin gwiwar wani bankin kasuwanci.

Sarkin na Kano ya kai ziyara fadar basaraken na Jos ne a cikin ziyarar da yake yi a jihar.

Jacob Gyang Buba kuma shi ne shugaban Majalisar Sarakunan jihar Filato.