Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero sun halarci bikin bude Masallacin Adogba da ke birnin Ibadan, wanda Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya sake ginawa da kudin aljihunsa.
Gwamnan, wanda ba Musulmi ba ne, ya dauki nauyi sake gina masallacin ne bayan an rusa shi a shekarar 2020 a dalilin aikin gina wata tashar mota a babbar hanyar Iwo-Road a Ibadan.
Sabon masallacin da gwamnan ya cika alkawarin ginawa bayan an canza masu matsuguni zuwa inda yake a yanzu, ya hada da makarantun Islamiya da na boko da dakunan karatu da bincike na zamani a harabarsa.
- Ban ga dalilin ta da jijiyar wuya don mun gayyaci Zakir Naik ba —Sarkin Musulmi
- Sarkin Kano ya je ta’aziyyar basaraken Kasar Ibira a Kogi
Ga yadda bikin ya gudan cikin hotuna: