Wata gobara ta salwantar da rayukan miji da matarsa da kuma jikansu a unguwar Ori-Eru da ke unguwar Idikan a garin Ibadan a Jihar Oyo.
Gobarar wacce ta tashi a wani ginin bene, ta afku ne da sanyin safiyar Juma’a, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito.
- ’Yan Arewa sun ƙi amfani da damar da suka samu na shugabancin Najeriya – Dogara
- Kwastam ta kama tabar wiwi, man fetur da kuɗinsu ya kai N229m a Ogun
Babban Manajan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo, Yemi Akinyinka, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Ibadan.
Akinyinka ya ce, hukumar ta samu kiran gaggawa game da tashin gobarar da ƙarfe 3:46 na daren ranar Juma’a daga wani Hassan kuma nan take ta tura jami’anta zuwa wurin.
“Da isowarmu, mun tarar da wani bene mai hawa shida yana cin wuta. Nan da nan muka zage damtse, kuma an kashe gobarar gaba ɗaya,” in ji shi.
Akinyinka ya tabbatar da cewa mutum uku – miji, matarsa, da jikansu – sun rasa rayukansu a tashin gobarar, yayin da aka ceto wasu biyar da ransu daga ginin.
Ya ƙara da cewa an kuɓutar kadarorin da ke ginin benen na ƙasa da na kusa da su daga gobarar.