✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban karamar hukuma ya rasu ana dab da rantsar da shi a Yobe

Ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya.

Allah Ya yi wa sabon shugaban kwamitin rikon kwarya na Karamar Hukumar Karasuwa, Lawan Gana Karasuwa rasuwa, kasa da sa’a 24 kafin a rantsar da shi.

Daraktan yada labarai na Gwamnan Jihar Yobe, Mamman Muhammad, ya sanar cewa Lawan Gana Karasuwa ya rasu ne a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Nguru bayan gajeriyar rashin lafiya.

Aminiya ta gano cewa Gana ya rike mukamin shugaban Karamar Hukumar Karasuwa na tsawon watanni shida kafin daga bisani gwamna Mai Mala Buni ya rushe kwamitin.

Daga nan aka sake nada shi a matsayin shugaban riko na karamar hukumar.

Yana daga cikin shugabannin kwamitin riko na kananan hukumomi 17 da za a rantsar da su a ranar Juma’a.