Allah Ya yi wa Sarkin Ibadan (Olubadan), Oba Owolabi Olakulehin, rasuwa a yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan cikarsa shekara guda a bisa karagar mulki.
Shaidu sun bayyana cewa Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga Mahaliccinsa ne a safiyar ranar Litinin ɗin, 7 ga watan Yuli, 2025.
Ya rasu ne kwana uku bayan kammala bikin cikarsa shekara 90 a duniya.
Oba Oluwabi, wand aka haifa a shekarar 1935, ya hau karagar mulki ne a watan Yulin shekarar 2024, inda ya gaji mariya Oba Lekan Balogun.
Rasuwar tasa ta auku ne sa’o’i kaɗan kafin fara taron ’yan jarida da aka shirya domin bayyana tsare-tsaren bukukuwan cikarsa shekara guda a kan mulkin Masarautar Ibadan.