Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu.
Ya rasu ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Afrilu, 2025, yayin da yake jinya a ƙasar waje kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.
- An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai
- Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi
Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa, inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki kuma jajirtacce.
Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda Oladunjoye ke yi wa aiki a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce rasuwarsa babban rashi ne.
Ya ce Oladunjoye mutum ne mai kishin jam’iyya, jajirtacce, kuma ya taka rawar gani wajen tallata APC a jihar.
Za a sanar da lokacin jana’izarsa daga baya.