✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Boko Haram ke kulla alaka da ’yan bindiga

’Yan bindiga daga Zamfara na zuwa Borno don samun horo a hannun Boko Haram.

A makon jiya ne aka samu rahoton bayanan sirri da ke nuna cewa ’yan bindiga daga Zamfara suna tafiya Jihar Borno domin samun horon ta’addaci a hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

Rahoton na PRNigeria, ya ce wadansu ’yan bindiga sun fara tafiya domin samun horon da ake zargin bangaren ISWAP na Boko Haram ne za su shirya.

– Boko Haram na rububin hada kai da ’yan bindiga

Jihohin da suka fi fama da ta’addancin ’yan bindiga masu garkuwa da mutane a yanzu su ne: Neja da Kaduna da Zamfara da Katsina da Sakkwato da Kebbi.

Kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad wadda aka fi sani Boko Haram da ta Daular Musulunci a Afirka ta Yamma (ISWAP) da Jama’atu Ansaril Muslimina Fi Biladis Sudan da aka fi sani da Ansaru sun baza komarsu, inda suke rububi tare da tsere wajen daukar ’yan bindigar tare da mayar da su cikinsu.

Mutanen gari da wasu majiyoyi da masana da Aminiya ta zanta da su, sun bayyana cewa tuni kungiyoyin Boko Haram din suka fara samun nasara, inda wadansu ’yan bindigar suka fara yi musu mubaya’a.

Jihohin shida da suka fi fama da ta’addancin ’yan bindiga masu garkuwa da mutanen suna da fadin kasa murabba’in kilomita 249,143, wanda ya fi girman kasar Birtaniya baki daya, kuma yawancin yankunan manyan dazuzzuka ne sai kuma kauyuka.

Wani masani a kan harkokin ta’adanci a Cibiyar Bincike ta Tony Blair, Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana wa Aminiya cewa yadda Boko Haram take kutsawa cikin ’yan bindigar abin tsoro ne.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ba ta ce komai ba a lokacin da Aminiya ta nemi jin ta bakinta a kan wannan labari.

SAURARI: Abin da ke saka wa ‘yan Najeriya shakku kan COVID-19:

– Yadda suke hadakar

Majiyoyinmu sun bayyana cewa tun da dadewa kafin rasuwar Abubakar Shekau, bangarensa da bangaren ISWAP suke ta kokarin neman gindin zama a yankin Arewa maso Yamma da Jihar Neja domin raba hankalin jami’an tsaro da suka fi mayar da hankali a kan jihohin Borno da Yobe inda Boko Haram ta fi karfi.

Kungiyar ta’addanci ta Ansaru, wadda tun bayan da aka fafattake ta daga Okene a Jihar Kogi ta dan lafa, an samu labarin cewa tana tare ne da tawagar ’yan bindigar da suke karkahin jagorancin Dogo Gide a dajin Kuyambana da yake tsakanin jihohin Neja da Kaduna da Zamfara.

“Tun shekarar 2012 Ansaru take yankin Arewa maso Yamma. Manufarsu ita ce su samu mabiya a yankin, wanda hakan ya sa suke yin wa’azi da Fulatanci, sannan suke ba da rancen tallafin kudi ga manoma,” inji Bulama Bukarti.

Aminiya ta gano cewa Dogo Gide yana da alaka mai karfi da Ansaru, inda suka girmama shi kasancewar yana da karfin iko a cikin ’yan bindingar.

Wani rahoto na wata cibiya mai suna Crisi Group, ya gano cewa ISWAP tana samun shiga yankin Arewa maso Yamma ta hanyar ba da tallafi ciki har da alawus na wata-wata ga wadanda suka bi ta.

Majiyoyinmu sun bayyana cewa ’yan ta’addan suna shiga cikin ’yan bindigar ne ta hanyar ba su tallafin makamai da horo da kuma wa’azi.

A wasu lokutan kuma, sukan aika musu da masu wa’azi na musamman domin su jawo hankalinsu ta hanyar amfani da bayanan cewa ba a yi wa makiyaya adalci a kasar nan.

Wata majiya ta jami’an tsaro ta shaida wa Aminiya cewa a kwanakin baya ma wadansu ’yan bindiga da ake kyautata zaton na Boko Haram ne sun zo a motoci kirar Hilux guda bakwai, inda suka sauka a Dajin Dunburum da ke Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara, inda wani jagoran ’yan bindiga, Alhaji Shingi ya sauke su, kuma tuni suka kafa sansaninsu a yankin.

– Yankunan da suka fi shiga

Aminiya ta samu bayanin cewa Boko Haram ta kafa sansani a Dajin Wawa da ke Jihar Neja, inda take samun kari mambobi daga sansanonin ’yan bindiga da suke Zamfara.

Wani Bafulatani da yake da ’yan uwa masu zama a yankin, ya ce Boko Haram din ne take yanke hukunci a kotunan da ta kafa a yankunan.

Dogo Gide ne yake jagorantar ’yan ta’addan yankin na Wawa, inda karfin ikonsa ya kai har Dajin Dangulbi da ke Jihar Zamfara da wasu yankuna a yankin Zuru da ke Jihar Kebbi.

Idan ba a manta ba, Dogo Gide ne ya jagoranci sulhun sako ’yan makarantar Kagara da aka sace, kuma shi ne wanda ake zargi da kashe dan bindigar nan Buharin Daji.

Majiyoyi sun ce Ansaru ta fi karfi a Dajin Kuyambana a yankin Birnin Gwari da wasu dazuka a kananan hukomomin Igabi da Giwa a Jihar Kaduna da Shiroro da Kagara a Jihar Neja.

A jihohin Zamfara da Sakkwato, ’yan ta’addan suna jawo hankalin ’yan bindigar ne ta hanyar kawo musu makamai daga Jamhuriyar Nijar.

Hakan ne ya jawo musu ’yan bindiga da suke addabar yankunan Sabon Birni da Isa a Sakkwato da Zurmi a Zamfara da wasu yankunan Katsina.

Sai dai wadansu ’yan bindigar sun ki amincewa da tayin na Boko Haram kamar yadda Aminiya ta samu labari.

– ’Yan bindiga sun fara amfani da ‘shari’a’ a yankunan

Wadansu daga cikin ’yan ta’addan da suka yi mubaya’a ga

Boko Haram sun fara amfani da dokokin ‘shari’a’ wajen hukunci a yankunansu.

Aminiya ta gano cewa wadansu daga cikinsu sun haramta zina da shan kayan maye da satar shanu da sauransu.

A wata murya da aka dauka an ji Dogo Gide yana cewa yana da makarantar Islamiyya da yake sa daliban da aka sato.

Ya sha alwashin zai mayar da su mayaka, sannan ya aurar da su, a wani irin salo da aka san Boko Haram ke yi.

A yankunan Zurmi na Jihar Zamfara da Kagara na Jihar Neja, wani jagoran ’yan bindiga mai suna Turji ma yana amfani da irin wannan salo, inda ake cewa shi ma yana da alaka da Boko Haram.

– Akwai matsala idan suka hada kai – Bulama Bukarti

Da yake bayani kan lamarin, Audu Bulama Bukarti ya ce samun hada-ka a tsakanin Boko Haram da ’yan bindigar abin tsoro ne, inda ya bukaci hukumomi su yi duk mai yiwuwa domin hana hakan tabbatuwa.

“Da farko dai Boko Haram za su kara musu kwarin gwiwa da hujjojin kashe mutane da sauran ta’addanci (da sunan addini).

“Idan wanda yake kashe mutane ya samu hujja da fahimtar cewa kashe-kashen nan jihadi ne, abin zai kara ta’azzara.

“Sannan haduwarsu da Boko Haram za ta taimaka musu wajen kara daukar matasa su shigo cikinsu,” inji shi.

Kakakin Hukumar DSS, Peter Afunaya bai amsa wayar da Aminiya ta yi masa domin jin ta bakinsa kan lamarin ba, sannan bai maido da sakon waya da wakilinmu ya tura masa ba.

– Kungiyoyin ta’addanci da suke barbarar ’yan bindigar

Ansaru ta fi karfi a jihohin Kogi da Neja, inda harkokinta suka fi karfi wajen garkuwa da mutane, musamman ’yan kasashen waje.

Aminiya ta gano cewa akwai akalla kungiyoyin ta’addanci uku a tsakanin jihohin Kaduna da Zamfara da Neja.

Bayan Ansaru, akwai Kungiyar Darul Islam, wadda ta fi karfi a Jihar Neja, kuma akwai mambobinta a Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa.

A shekarar 2009 ne aka fara samun labarin Darul Islam, bayan ’yan sanda sun fatattake su a yankin Mokwa na Jihar Neja, inda a lokacin ’yan sanda suka ce daga cikin wadanda suka kama akwai ’yan kasashen waje irin su Chadi da Kamaru da Nijar.

Boko Haram da ISWAP sun fi karfi a jihohin Borno da Yobe, amma bayanai sun ce suna shiga yankin Arewa maso Yamma ne domin raba hankalin jami’an tsaro da kuma samun karin mambobi.

A ranar 7 ga Yulin bara ce Boko Haram ta gudanar da Sallar Idi a wani daji da ke Jihar Neja, inda ta aike da gaisuwa zuwa ga Shekau, wanda hakan ya tabbatar da kasancewarsu a yankin.

– Tuntuni aka ankarar da gwamnoni kan kasancewar ’yan ta’addan a jihohinsu – Kukasheka

Da yake bayanin kan lamarin, Birgediya Janar, Sani Kukasheka Usman (mai ritaya) ya ce ’yan ta’adda na neman hadaka da ’yan bindigar ne don su kara karfin ikonsu.

Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Kasan wanda yake da masaniya a kan yaki da Boko Haram, ya ce ba tun yau ba aka fara ankarar da gwamnoni kan kasancewar Boko Haram a wasu jihohi, amma suka ki yin komai.

“Gwamnonin sun fi son su yi maganin abu na dan lokaci kawai,” inji shi.

Ya kara cewa yawancin matsalolin suna bukatar natsuwa wajen fuskantarsu, ba yadda wadansu gwamnonin suka so a yi ba cikin gaggawa.

Kukasheka ya alakanta lamarin da rashin samun hadin gwiwa a tsakanin gwamnotoci a dukkan matakai da kuma mutanen gari, wanda hakan ke jawo boye bayanan sirri wadanda za su iya taimaka wa jami’an tsaro su dakile ’yan ta’addan cikin sauri.

%d bloggers like this: