Wani magidanci mai suna Sa’idu Muhammad ya gurfanar da tsohuwar matarsa a gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna bisa zargin ta da yin aure a kan aurensa tare da neman kotun da ta dawo masa da matarsa.
Mai karar ya shaida wa kotu cewa sun kwashe shekara 20 da matar tasa mai suna Fatima Ali, inda daga bisani wata tafiya ta kama shi zuwa kasar Ghana, inda ya kwashe shekara 20 bai dawo ba.
- Hanifa: Matar Abdulmalik za ta yi wani jawabi a gaban kotu
- Na shiga damuwa kan rashin zuwa Zamfara —Buhari
- Hanyoyin kasuwanci da samun kudi don matasa
A cewarsa bayan ya dawo ne ya sami labarin cewa matar tasa ta yi sabon aure har ma tana gidan mijinta.
Lokacin da kotu ta bi bahasin yadda lamarin ya faru daga matar mai suna Fatima, ta shaida wa kotu cewa ganin cewa an dau tsawon lokaci tsohon mijin nata bai dawo ba hakan ya sa ta je wata kotu ta nemi a sake ta.
A cewarta kafin kotun ta yanke hukunci a kan lamarin sai da mahaifin mijin nata, (wanda a yanzu ya rasu) ya ce tun da kotun tana jinkiri to shi ya saki auren dan nasa a madadinsa. “Hakan ya sa na yi aurena,” inji ta.
Sai dai matar ta shaida wa kotun cewa tun da a yanzu tsohon mjinta ya dawo to ta fi son ta koma hannunsa.
Lokacin da kotun ta waiwayi sabon mijin wato Amadu Sani, ya shaida wa kotun cewa a yanzu ya fara auren matar tasa don haka ba zai sake ta ba.
Alkalin kotun, Dokta Bello Musa Khalid ya ce kotu za ta rubuta takarda zuwa kotun baya domin jin karin bayani.
Haka kuma ya bayar da umarnin cewa matar ta koma gidan iyayenta kuma kada sabon mijinta ya sake kusantarta har sai kotun ta bayayna matsayarta a kan shari’ar.
Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu na bana.