’Yan sanda sun cafke wani magidanci bisa zargin sa da kashe matarsa mai juna biyu a kan gadon asibiti.
An tsare magidancin ne bayan da ya tumbuke na’urar Oksijin da aka sanya wa matar tasa a lokacin da aka kwantar da ita a asibiti.
- Yadda bakin ciki ya yi ajalin iyayen ’yan matan Chibok 17
- Ana gwabza fada tsakanin sojoji da Boko Haram a Borno
- Boko Haram ta sake kwace garin Damasak
“Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya ba da umarnin sashen binciken kisa ya bincike shi a Sashen Bincikin Manyan Laifuka (CID),” inji kakakin ’yan sandan Jihar Legas, Muyiwa Adejobi.
Ya ce an kwantar da matar a gadon asibiti ne sakamakon matsalar juna biyun da take dauke da shi, lokacin da mijin ya faki ido ya tumbuke mata Oksijin din, har ta kasa numfashi, daga baya ta rasu.
Ana kuma zargin cewa kafin faruwar lamarin, mutumin na da dabi’ar yawan dukan matar tasa.