✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya gina gida mai jujjuyawa don burge matarsa

Na gaji da korafin matata kan in sake gyara fasalin gidanmu a kai-a-kai.

Wani magidanci mai suna Bojin Kusic ya faranta wa matarsa rai, bayan da ta yi fatan ganin sauyin fasalin gidansu.

Mutumin dan Bosniya, ya gina gida mai juyawa ne wanda yake ba da damar kallon fitowar rana da faduwarta a lokaci guda da kuma masu wucewa ta gaban gidan.

Bojin Kusic, mai shekara 72, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, “Na gaji da korafin matata kan in sake gyara fasalin gidanmu a kai-a-kai.

“Zan gina mana gida mai jujjuyawa don a iya jujjuya shi yadda ake so.” Bojin Kusic, ya bayyana haka ne a kafar labaran ne lokacin da yake tsaye a gaban gidan.

Bojin Kusic yana dawo gida tare da wani jikansa
Hoton gidan da Bojin Kusic ya gina wa matarsa don ya burge ta

Sabon fasalin gidan nasa yana jan hankalin maziyarta.

Gidan wanda yake a wani fili a Arewacin Bosniya kusa da birnin Srbac, yana da tsawon mita bakwai wanda Kusic ya tsara, da yake kallon gonakin masara da filayen noma.

“Gidan zai iya juyi a cikin sa’o’i 24 idan an rage saurin juyin gidan mafi karanci, yayin da yake juyi mafi sauri a cikin dakika 22,” inji Kusic.

Sai dai matarsa ta ki yin magana game da sabunta fasalin gidan.

Kusic ya ce, wadansu Amurkawa ’yan asalin Sabiya ne suka ba shi kwarin gwiwa wadanda suka hada da Nikola Tesla da Mihajlo Pupin.

Ya ce kasancewarsa daga cikin matalauta ba tare da yiwuwar samun ingantaccen ilimi ba, hakan ya tilasta masa neman hanyoyin yin abubuwa da kansa.

Ya kara da cewa, shi ne ya gina gidan gaba daya da kansa, kuma ya dauki shekara shida kafin kammala gidan da zai iya jure girgizar kasa fiye da gidajen da suke tsaye kawai.