Wutar lantarkin Najeriya ta sake ɗaukewa gaba ɗaya, bayan ta ragu daga megawat 3,594.60 da tsakar daren Litinin zuwa megawat 42.7.
Injinan da suke Jihar Delta da ke samar da megawat 41 ne kawai suke aiki ya zuwa karfe 12:00 na ranar Talata, yayin da tashar lantarki ta Afam ke samar da megawat 1.7.
- Saudiyya ta ware wa Najeriya kujeru 95,000 a Aikin Hajjin 2024
- Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin dubu 390
Hakan na zuwa ne kasa da kwana biyar bayan injinan lantarkin kasar sun sake durkushewa na sama da sa’o’i 12, lamarin da ya jefa ilahirin kasar cikin duhu.
Har zuwa yanzu dai babu gamsasshen bayani kan musabbabin ɗaukewar wutar, amma Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce matsalar gobara ce ta haddasa matsalar.
A wasu jerin saƙonni da ya wallafa a dandalin X (Twitter), Ministan ya ce wuta ce ta tashi a layin injinan da ke Kainji/Jebba masu karfin megawat 356.63.
“Amma muna kan aiki ba dare ba rana wajen dawo da lantarkin. Mun sami nasarar kashe wutar kuma nan ba da jimawa ba lantarkin za ta dawo. Muna ba ’yan Najeriya hakuri,” kamar yadda Ministan ya wallafa a dandalin X.