✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin dubu 390

Hakan ya faru ne sakamakon karuwar kudin da kaso 75 cikin wata uku

A daidai lokacin da jimillar bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 87.4, yanzu ke nan ana bin kowanne ɗan ƙasar Naira 390,517.17.

A cewar Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS), yawan bashin ya karu da sama da kaso 75 cikin 100 a cikin watanni uku kacal.

NBS ta ce ya zuwa karshen wata shidan farkon 2023, bashin ya yi tashi gwauron zabo zuwa sama da Naira tiriliyan 87.4.

Bincike ya nuna bashin da aka ci a cikin gida ya kai tiriliyan 54.13, yayin da na kasar waje ya haura tiriliyan 33.25.

Idan aka raba adadin kudin ga yawan al’ummar Najeriya, wanda wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan yawan jama’a ya ƙiyasta cewa ya zuwa tsakiyar shekarar za su kai 223,804,632, za a sami wancan adadin.

Mun raba tiriliyan 87.4 ga yawan ’yan Najeriya su 223,804,632, kowa zai zama ana bin shi bashin 390,519.

Yadda bashin ya ninku a cikin wata uku

Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) a cikin wani rahoto ranar Alhamis ta ce bashi ya hada har da na Naira tirliyan 22.71 da Gwamnatin Tarayya ta ciyo daga Babban Bankin Najeriya (CBN).

A cewar DMO, “Jimillar bashin da ake bin gwamnati a Najeriya ya zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2023 ya kai tiriliyan 87.38. Hakan ya haɗa da wanda Gwamnatin Tarayya da Jihohi 36 da ma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kazalika, bashin da ake bi na cikin gida ya kai tiriliyan 54.13, sai kuma wanda aka ci daga ketare da ya kai tiriliyan 33.25.