Dubban ’yan Najeriya da ke da niyyar tafiya Umrah a wannan wata na Ramadana babu lallai burinsu ya cika saboda rashin biza daga kasar Saudiyya.
Wannan ya biyo bayan wani sabon tsarin bayarda biza da ƙasar ta Saudiyya ta fito da shi.
Kawo yanzu cikin waɗanda suka biya kuɗin tikiti da biza ya ɗuri ruwa.
Tuni ta bayyana ga masu jiragen sama cewa bana ba za su samu kasuwa kamar yadda suka saba yi ba.
Kazalika, masu masaukin baƙi da ke da ɗakunan haya na masu Umara da aikin Hajji za su samu nakasu a abin da za su samu.
- An yi wa mara lafiya dashen ƙodar alade a Amurka
- ‘Ana bai wa waɗanda ba su cancanta ba kwangiloli na miliyoyin Naira a Kano’
Mun gano cewa kawo yanzu an soke tashin waɗansu jirage zuwa kasa mai tsarki, wasu kuma an canza musu lokacin tashi.
Wata majiya ta shaida mana cewa akwai jirgin da ya kamata ya tashi da maniyyatan Umrah mutum kusan 300 amma bai tashi ba.
Rashin tashin jirgin zuwa kasa mai tsarki ya samo asali ne saboda rashin samun bizar da dama daga cikin waɗanda ya kamata a tashi da su.
Watan Ramadana lokaci ne da dubban ‘yan Najeriya ke tafiya Umrah domin falalar da ke tattare da yin Umrah a lokacin Azumi.
Amma abin da ya tabbata shi ne, a bana da dama ba za su samu damar zuwa ba.
Babangida Da Azumi, wani da ya jima yana tafiya Umrah ya bayyana mana cewa, ya saba yana tafiya Umrah tare da wasu mutum shida.
Amma a bana ko mutum ɗaya bai samu biza ba a cikinsu, wanda hakan ya ɗaga musu hankali.
Sadi Hamisu Ala ya ce, “a ranar 15 ga watan Maris ya kamata mu tashi, amma lissafi ya kwace saboda ba a shirya bizar ba, mu takwas muka sayi tikiti watanni bakwai da suka gabata, muna ganin biza za ta samu kamar kowace shekara amma har yanzu shiru.”
‘Sabon tsarin Saudiyya ya janyo matsalar’
Masu kamfanonin taimakawa maniyyata samun biza sun zargi sabon tsarin biza da kasar Saudiyya ta fito da shi a matsayin dalilin da ƙasar ta kasa bai wa maniyyatan biza.
Shugaban kungiyar masu hada-hadar tikitin jirgi da bizar tafiya aikin Umrah a jihar Kano Haruna Ismail, ya bayyana cewa, “wannan sabon tsarin na bizar wata uku da damar zama a kasar Saudiyya na sati biyu kaɗai ne dalilin da samar da bizar ke tafiyar hawainiya.
Wasu maniyyatan da suka samu biza tun a watan bakwai sun ajiye ba su tafi ba sai a watan Ramadan.
Ya ce “wannan sabon tsarin ya zo da matsaloli da dama, ta yadda waɗansu sun karbi biza tun a watan 7, wasu kuma sun je sun yi zamansu a can saboda ba su fahimci ainihin abin da tsarin ke nufi ba.”
Abdulaziz Sabitu Muhammed mataimakin shugaban kungiyar masu hada-hadar tikitin jirgi da bizar tafiya aikin Umrah a jihar Kano ya bayyana cewa, “akwai maniyyatan aikin Umrah dubu bakwai da suka samu biza amma ba su tafi ba, saboda suna da damar jinkirta tafiya har tsawon watanni uku.”
Ya kara da cewa, akwai maniyyata 260 da sun samu tikitin jirgi amma 40 ne kaɗai suka samu biza.
Ya ce, “kididdigar da muka yi a shekarar da ta gabata, mutum miliyan 25 suka yi Umara, miliyan uku kuma suka yi Umara a watan Ramadan, amma a bana, saboda sabon tsarin bizar da aka yi, mutane da yawa sun ci gaba da zama a Makka.
“Akwai mutanen da suka tafi tun Sha’aban suna can har bayan sun yi Umara.