✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana, zai nazarci irin waɗannan ƙalubale da matasa ke fuskanta.

More Podcasts

A yau, da dama daga cikin matasan Najeriya na fama da matsaloli masu tarin yawa, musamman wajen ciyar da kansu da biyan buƙatunsu na yau da kullum.

Wannan na faruwa ne sakamakon halin da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki, rashin aikin yi, da kuma tsadar rayuwa.

Wasu daga cikin matasan sun kammala karatu, wasu kuma suna da sana’o’in hannu, amma duk da haka, rashin samun aikin da zai biya musu buƙatunsu yana ƙara jefa su cikin mawuyacin hali.

Wannan matsala na ci gaba da haddasa damuwa ga matasan ƙasar, inda da dama daga cikinsu ke fuskantar ƙuncin rayuwa sakamakon rashin tabbas a makomarsu.

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana, zai nazarci irin waɗannan ƙalubale da matasa ke fuskanta, musamman a matakin farko na rayuwarsu.

Domin sauke shirin, latsa nan