Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha.
Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya.
- Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi
- Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha.
Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe mata da kuma kananan yara a Ukraine.
Sakataren ya kuma kara da cewa a yanzu zabi ya rage ga Rasha na ta amince da kudurin ko kuma akasin hakan.
Sakataren ya kuma kara da cewa a yanzu zabi ya rage wa Rasha, inda kowanne lokaci daga yanzu ne ake shirin miƙa mata ƙunshin matsayar da aka cimma a wannan taro na Jedda don nazartarta da kuma yiwuwar aminta da ita ko akasin haka.
Wasu majiyoyi sun bayyana yiwuwar Donald Trump ya tattauna da Vladimir Putin a cikin makon nan bayan matakin na Ukraine dangane da amincewa da tayin Washington kan tsagaita wuta a yaƙin ɓangarorin biyu.
Har ila yau, Amurkar ta kuma amince ta koma bai wa Ukraine din bayanan sirri da kuma tallafin tsaro.