✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci

Gwamnatin Jamus ya yi marhabin da yarjejeniyar kasuwanci da aka cimma tsakanin Washington da Beijing a birnin Landan.

Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da ke kawo karshen zaman tankiyar da aka soma tsakanin kasashen biyu tun bayan hawan Donald Trump karagar mulki.

Kasashen biyu sun cimma matsaya a kan kan cinikin wani rukini na ma’adinai da Chinar ke fitarwa, wadanda ake kira da sunan Terres Rares, wadanda ake yi amfani da shi wajen samar da lantarki da kuma makamashin da ake sabbintawa.

A baya a taron kasar Switzerland, Washington ta amince da rage haraji kan kayayyakin kasar China daga kashi 145 zuwa kashi 30 cikin 100, don musanya makamancin wannan mataki da Beijing ta dauka daga kashi 125% zuwa 10% kan kayayyakin Amurka, na tsawon kwanaki 90.

Shugaban Gwamnatin Jamus, Frederich Merz, ya yi marhabin da yarjejeniyar kasuwanci da aka cimma tsakanin Washington da Beijing a birnin Landan na Birtaniya.

Merz ya ce yana maraba da wannan yarjejeniya, kuma yana matukar Kungiyar Tarayyar Turai za ta yi nasara wajen rage rikice-rikicen kasuwanci da Amurka.

A watan Mayun da ya gabata ne China da Amurka suka cimma yarjejeniyar jinkirta aiwatar da sabon tsarin biyan harajin da suka lafta wa juna har sai bayan kwanaki 90, matakin da tun a lokacin aka yi tsammanin zai iya kawo karshen zaman tankiyar da ake yi tsakanin kasashen biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Sai dai a farkon makon nan ne China ta tabbatar da cewa wakilanta za su gana da takwarorinsu na Amurka a kasar Birtaniya.