✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China

Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar…

Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar China.

Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa jirgin wanda ke dauke da fasinjoji, ciki har da kananan yara biyar da kuma ma’aikatan jirgi su shida, ya fadi ne ranar Alhamis ba tare da ko mutum daya ya rayu ba.

“Ma’aikatan ceto sun gano wasu sassan jirgin na ci da wuta,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito jami’an ceton na cewa.

Reuters ya kuma ce jirgin wanda mallakin kamfanin Angara Airlines ne, ya fadi ne a kusa da Tyndra, wani gari da ke yankin na Amur, bayan hanyar da yake magana da masu kula nda zirga-zirgar jirage a sararin samaniya ta katse.

Kazalika, kamfanin dillancin labaran Rasha na Interfax, ya ce jirgin ya fadi ne a yunkurinsa na sauka a karo na biyu bayan ya kasa sauka a karo na farko a filin jiragen saman a Tyndra.

Kamfanin ya kuma rawaito cewa rashin kyawun yanayin gani ne a lokacin sauka ne ya haddasa hatsarin.

Sai dai bayan faduwar jirgin yak ama da wuta, kuma ana zargin babu ko mutum daya da ya rayu, kamar yadda wani faifan bidiyo a wajen da jirgin ya fadi ya nuna

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, kamfanin na Angara bai kai ga fitar da cikakken bayani kan musabbabin hatsarin ba.