✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya

A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari.

Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya.

A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina.

Bayan rasuwar ce gwamnoni da wasu fitattun ’yan siyasa da a halin yanzu suna ƙasa mai tsarki suka kai wa Gwamna Radda ziyara domin jajanta masa dangane da wannan babban rashi.

Daga cikin gwamnonin akwai Mohammed Umar Bago na Jihar Neja, da Farfesa Babagana Zulum na Jihar Borno da Gwamna Uba Sani na Kaduna, da Dauda Lawal Dare na Zamfara da kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe

Sauran fitattun ’yan siyasar da suka ziyarci Gwamna Radda sun haɗa da Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da tsohon Gwamnan Bauchi, Ahmed Mu’azu.

Akwai kuma fitaccen attajirin nan kuma ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal da kuma tauraron tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa da su ma suka jajanta wa gwamnan a kan rashin.

Dukkansu sun bayyana alhini tare da roƙon Allah Ya jiƙan Hajiya Safara’u Ya sa ta huta.