✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wata mata ta sayar da ’ya’yanta biyu a Ogun

Ta ce halin yau ne ya sanya ta aikata hakan.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta kame wata matar aure ’yar shekara 35 mai suna, Blessing Ebuneku Agoro, kan zargin sayar da ’ya’yanta mata biyu a kan Naira dubu uku.

Ta ce ‘halin yau’ wajen kula da su bayan maigidanta ya bar ta da su, shi ne ya sa ta aikata hakan.

Aminiya ta gano cewa wacce ake zargin da ta sayar da babbar diyar Semilore Agoro (mai shekara hudu) da Deborah Agoro (‘yar shekara biyu) an kama ta ne bayan da mijinta, Oluwaseyi Agoro ya kai karar ta gaban ’yan sanda.

Mijin ya fada wa ’yan sandan cewar ya yi wani bulaguro na dan lokaci, amma bayan komawarsa gida ranar 8 ga watan Yuni bai tarar da ’ya’yansa nasa guda biyu a gidan ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya fada wa manema labarai ranar Lahadi cewa bayan samun rahoton, Babban Jami’in ’yan sandan yankin, CSP Alabi Akinjide, ya umarci jami’ansa da su kamo matar.

A cewarsa, bayan da aka titsiye wacce ake zargin ta bayyana cewa mijin nata ya shekara biyu da barin gida, lamarin da ya sanya ta shiga cikin kuncin kula da ’ya’yan nasu tare da wadansu ’ya’yan biyu da ta haifa da wani mijin na daban.

“Ta shaida mana cewa a lokacin da take tunanin me ya kamata ta yi, wani mai suna Kolawole Imoleayo ya kai ta wajen wadansu ma’aurata a Fatakwal masu tsananin bukatar haihuwa inda ta sayar musu da ’ya’yan guda biyu a kan Naira dubu dari uku,” a cewarsa.

A cewar jami’in, bayanin nata ya taimaka wa ’yan sandan kame dillalin da ya shiga tsakani, Kolawole Imoleayo, sannan dukkansu suna, “taimaka wa ’yan sandan a binciken da suke yi, sannan za su tabbatar da an ceto wadannan ’yan matan domin dawo da su gaban iyayensu nan ba da jimawa ba.”