✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wata mata ta kashe ’ya’yan kishiyarta 4 da guba

An kama ta kan zarin sanya wa yaran guba a cikin shayin da ta hada musu.

’Yan sanda sun yi ram da wata mata kan zargin kashe ’ya’yan  kisiyarta su hudu ta hayar sa musu guba a abin karin kumallonsu a Jihar Yobe.

Matar mai shekara 22 da ke zaune a unguwar Makara Huta da ke garin Fataskum, ana zargin ta ne da sanya wa ’ya’yan uwargidarta hudu gubar ce a safiyar Juma’a.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya ce binciken da aka gudanar ya tabbatar musu da cewa bayan yaran sun sha shayi da kishiyar mahaifiyar tasu ta hada musu da safe ne aka gano sun sha guba.

Ya shaida wa manema labarai ta wani sako da ya fitar cewa, “Nan take aka hanzarta kai yaran Asibiti Kwararru na Fataskum a safiyar ta Juma’a 17 ga watan Satumba, 2021.”

Dungus, ya ce uku daga cikin yaran sun rasu ne a lokacin da ake jinyar su, na hudun kuma yake cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

“Mijin matar dai shi ne ya kai rahoton faruwar haka a ofishin ’yan sanda da misalin karfe daya na rana,” inji sanarwar.

Ya kara da cewa yaran da suka rasun sun hada da mata biyu da maza biyu, kuma shekarun bakwai ne zuwa 12.

“Tuni aka ci gaba da gudanar da bincike a yankin da lamarin ya faru don daukar matakin da ya dace”, inji shi.

’Yan jarida sun yi dafifi a Asibitin Kwararru da ke garin na Fataskum don daukar hoto, amma Mataimakin Daraktan Lafiya na asibitin ya hana su, inda ya ce sai sun samu izini daga ma’aikatar lafiya da ke garin Damaturu, hedikwatar jihar ta Yobe.