Wani matuƙin Keke-Napep a birnin Jalingo na Jihar Taraba, Muhammed Jibo, ya mayar da tsintuwar naira miliyan biyu da dubu ɗari huɗu da wani fasinja ya manta a cikin babur dinsa.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa wani mai suna Ghali Abdulhamid shi ne fasinjan da ya manta da jakar a lokacin da ya shiga Keke-Napep ɗin daga Kasuwar Jalingo.
Sai dai Jibo bai lura da jakar ba har sai da ya ɗauki wasu yara ’yan makaranta da suka ankarar da shi cewa ga jakarsa a kujerar baya.
Cikin mamaki Muhammed Jibo ya budye jakar bayan ya ajiye yaran, sai ya ga tsabar kuɗi har naira 2,450,000.
- An yi wa Bajamushe allurar Covid-19 sau 217 ba ta yi tasiri ba
- Ranar Mata Ta Duniya: Tallafin Da Zai Sa Mata Su Samu Cigaba
Nan take ya garzaya ofishin ƙungiyar masu Keke-Napep inda ya miƙa jakar da ke ɗauke da kuɗin ga manyan jami’an ofishin kungiyar tasu.
An gano adireshi da lambar wayar Ghali Abdul Hamid a jikin wata takarda a cikin jakar, kuma nan take aka gayyace shi ya zo ya bayyana adadin kuɗinsa aka miƙa masa abinsa.
Abdullahi Bello, shugaban ƙungiyar masu Keke-Napep reshen Jihar Taraba, ya shaida wa Aminiya cewa, kungiyar tana alfahari da gaskiyar da Jibo ya nuna ta miƙa kuɗin ga mai su, duk da cewa Keken da Jibo ke tukawa ma ba nasa bane, amma ya ci ƙarfin zuciyarsa ya bayar da kuɗin.
Muhammed Jibo dan asalin Jihar Gombe ne da ke aikin tuƙin Keke-Napep a Jihar Taraba.