Shekaru fiye da 20 na taɓa yin wani rubutu a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, da ya ja hankali inda daga baya aka sake buga shi a wasu jaridun Hausa.
Na yi rubutun ne kan illolin rabuwar aure, unda na duba ɓangarorin, rayuwar iyalin da aka rabu, musamman yara da kuma al’umma baki ɗaya.
A ƙarshe na nuna cewa, kuskuren da wasu ma’aurata ke yi shi ne suna duba matsalar kansu ce kawai ba sa tunanin abin da zai biyo baya, a kansu ko iyalin da za su bari cikin ƙunci.
Ba duka masu rabuwa ne, suke yanke hukunci ido rufe ba, wasu kan ɗauki lokaci suna nazari da auna abubuwan, har sai abin ya ƙure ne suke haƙura a rabu.
Wasu da ke rayuwar birane ko ’yan boko, har wajen ƙwararru suke zuwa, wato masana ilimin zamantakewa da sasanta ma’aurata, don neman shawara, ana kashe maƙudan kuɗi, don a kauce wa rabuwar a ceto aurensu.
Don haka ba za mu zargi duka masu rabuwar da rashin hankali ko tunani ba.
Mai yiwuwa abin da ya koro ɓera cikin wuta ne ya fi wutar zafi.
A makon jiya na samu labarin rabuwar auren da ya girgiza ni matuƙa, har iyali biyu, waɗanda a baya na san suna zaune lafiya da juna kuma cikin kyautatawa da haƙuri da juna.
Dukkansu sun kai kimanin shekara 18 ko kusa da haka, sun haifi yaran da suka fara mallakar hankalinsu. Amma sai muka ji ai sun rabu.
Ɗaya daga cikinsu wanda babu laifi idan na ambaci sunansu saboda labarin rabuwarsu ya yi yawo a jaridu da kafafen sadarwa, shi ne rabuwar auren Malam Al-Ameen Ciroma, ɗan jarida kuma jarumin finafinan Hausa da tsohuwar matarsa Wasila Isma’il, tsohuwar jarumar finafinan Hausa.
An ce aurensu ne mafi daɗewa a tsakanin jaruman masana’antar.
Kawo yanzu ba ni da masaniya kan dalilan rabuwar auren biyun, amma na san su kansu da suka rabu suna cikin wani yanayi na alhini da jujjuya abubuwan da suka faru, ko suka janyo rabuwar auren da za a iya cewa ta faru kamar mafarki.
Kamar yadda wasu ke cewa, yadda kowace halitta ke da rai haka aure na da nasa, idan ya zo ƙarshe babu makawa a rabu.
Za ta iya yiwuwa wani auren ya daɗe da rabuwa a zukatan ma’auratan, sai dai ba a yanke hukuncin sanarwa ba ne.
Wani auren kuma cike yake da zarge-zarge da aibata juna da ɓatanci da muzantawa, alhalin a baya an nuna wa juna soyayya da kula.
Wasu kuma dalilai ne na cin zarafi, zalunci da tozartawa, inda za a ce da wannan zama gara rabuwa.
Ko a nuna miji na duka da wulaƙanta matasa, ko tauye mata haƙƙoqinta da jefa rayuwarta a mummunan hali. Ko matar ce ke wulaƙanta mijin, aibata shi da cin zarafinsa.
Tun mijin na ɓoyewa har ya fitar da abin jama’a su fahimci uƙubar da yake ciki, amma ya danne saboda kada a ga gazawarsa.
Kamar yadda ake cewa, babu wani aure da ya yi kama da na wani, to, haka wajen rabuwa, za a tarar kowa da nasa dalilin.
Wani dalilin idan mutum ya ji sai ya yi dariya, domin batu ne da za a iya sasantawa cikin ruwan sanyi.
Wani abubuwa da dama ne aka riƙa tara su suka yi yawan da ba a iya warware su lokaci guda ba, sai dai a rabu idan da rabon sake komawa zaman aure a sake dawowa.
To, ko ma dai wane dalili ne, ko wane salo aka bi wajen rabuwar, za mu iya cewa rabuwar aure ba abu ne mai daɗi ba.
Saboda da zarar an yi aure an hayayyafa, ana ɗauka cewa an zama ɗaya, ko da an rabu.
Nauye-nauyen kula da yara da damuwa a kan karatunsu ko tarbiyyarsu, nan ma wata jarrabawar ce.
Su kansu yaran da aka raba wa hankali, ko aka
canza musu gida da makaranta da abokan rayuwa suna shiga cikin damuwa iri-iri.
Daga ciki akwai matsalar taɓarɓarewar tarbiyya, shaye-shaye, rashin ƙoƙari a makaranta da gudun shiga mutane.
Wani lokaci har da yawan zafin rai da shiga rigima, ko cin zalin wasu yaran.
Abin takaici ne yadda wasu musamman mata ke bayyana cewa, su ne suka nemi a raba auren don sun gaji da ganin baƙin ciki, sun gwammaci zaman zawarci da ci gaba da ganin wulaƙancin
da suke cewa suna gani a gidajen aurensu.
Alhalin kuwa addinin Musulunci ya tsawatar sosai kan matan da suke neman mazansu su sake su.
Wani lokaci kuma wasu ne a cikin mata ake samu su hure wa ’yan uwansu mata masu haƙurin zaman aure kunne cewa su bar gidan, in ba so suke rayuwarsu ta lalace ba.
Su riƙa karanto musu wasu abubuwa na rashin
tabbas da kwaɗaitar musu da rayuwar ’yanci da walwala a rayuwar zawarci.
Sai bayan sun fito daga gidan miji su tarar da rayuwar ba yadda suka zata ba.
Ƙalilan ne a matan da suke barin aurensu don
ganin suna shan wahala, suke sake samun wata dama ta sake yin aure ko kafa wani kasuwanci da zai riƙa kawo musu riba, suna kula da kansu, da ’ya’yansu.
Wasu sai dai gyaran Allah, rayuwar ƙara lalacewa take yi, har su gwammaci gara a ce sukoma ɗakin aurensu da zaman da suke yi na rashin tabbas, da yaudarar manema da ke jefa su a rayuwar zinace-zinace da sayar da mutunci.
Ban sani ba ko saboda ƙaruwar talauci da ƙuncin rayuwa ne, ya sa darajar aure ke ƙara zubewa a idanun wasu matan da ke ganin babu abin da aure ke tsinana wa rayuwar su in ba takaici da wahala ba.
Don haka za ka yi ta ji a maganganunsu da rubuce-rubucensu a Intanet, suna nuna gazawar aure da lalacewar maza, ko muguntarsu a cewarsu, wanda ke sa suna jin auren yana fita a ransu.
Kuma hakan ba ya rasa nasaba da yadda wasu mazan suke yi wa auren riƙon sakainar kashi da sake wa mata da ’ya’ya wahalhalun aure da kula da kansu.
Nauyin da sharuɗɗan kula da haƙƙoƙin aure suna kan maza ne. Amma yanzu a mafi yawan gidaje mata ake bari da ɗawainiya mazan sun juya musu baya, babu ko tallafawa.
Sai ka ga mace bazar-bazar kamar za ta yi hauka, tana fafutikar yadda za ta nema wa iyali abin da za su ci ko kuɗin makaranta, saboda uban wanda ya kamata ya zama jagora a gidansa halin yau da mutuwar zuciya sun sa ya yi watsi da buƙatunsu.
Don haka akwai buƙatar iyaye ma’aurata su dubi girman Allah, su tsaya su kula da gyaran gidajensu, a daina watsi da haƙƙoƙin da Allah Ya ɗora mana.
A riƙa tausaya wa juna ana kyautatawa, don a samu rabon duniya da Lahira.
Mata su daina sauraron waɗanda suka fitar da tsammani daga samun jin daɗin aure, masu hure wa wasu kunne don su bi sahunsu suna gantali a titi, wanda babu inda za su kai su sai halaka.
Abba Abubakar Yakubu, marubuci ne kuma ɗan jarida mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.
Za a iya samun sa ta: imel:[email protected].