✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al-Hilal ta yi wa Mbappe tayi mafi daraja a tarihi

Al-Hilal ta amince ta biya shi Yuro miliyan 13 a duk mako.

Kungiyar kwallon kafa ta Al Hilal da ke Saudiyya ta yi tayin sayen dan wasan gaban Paris St-Germain, Kylian Mbappe a kan €300m wato (£259m).

Dan wasan na Faransa mai shekara 24 na da sauran shekara daya kafin kwangilarsa ta kare a PSG kuma kawo yanzu ya ki sanya hannu domin tsawaita zamansa a kungiyar.

Hakan ya sa masu Club din na PSG suka dage don ganin lallai sun siyar da shi idan har ba zai amincewa da sabon kwantaragi ba, inda suka ce sun gwammace su karbi kasa da fam miliyan 155 da suka biya Monaco wajen dauko shi a shekarar 2017, domin kada ya wuce kyauta.

Yanzu dai PSG tana son sayar da Mbappe maimakon barinsa ya tafi salin-alin a bazara mai zuwa.

Hasalima kungiyar ta ki sanya shi a cikin tawagar da za ta tafi Japan da Koriya ta Kudu domin murza leda.

Rahotanni sun ce kungiyoyi irin su Tottenham, Chelsea, Manchester United, Inter Milan da Barcelona suna son daukar dan wasan.

Mbappe ya ce yana so ya ci gaba da zama a PSG har nan da shekara daya lokacin da kwangilarsa za ta kare. An yi amannar cewa yana son tafiya Real Madrid.

Sai dai kuma a yanzu Al-Hilal ta yi tayin bai wa Mbappe kwantiragin shekara guda kan dala miliyan 775 (€700m), kuma daga nan za ta ba shi damar cikar burinsa na tafiya Real Madrid.

Wannan ya nuna cewa kulob din na Saudiyya ya amince ya biya shi Yuro miliyan 13 a duk mako.