✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace mace mai shayarwa da danta a Neja

Maharan sun jikkata jami'an tsaro a yayin musayar wuta da suka yi a yankin Garin Gabas

An yi garkuwa da wata mata mai shayarwa tare da dan nata da take shayarwa da wani mutum guda a yankin Garin Gabas  da ke Jihar Neja.

Jami’an tsaro biyu kuma sun samu raunuka a yayin musayar wuta a lokacin da yan bindiga suka kai da misalin karfe 1 na dare a kauyen da ke Karamar Hukumar Rafi ta jihar.

Wani shaida ya ce, “’Yan bindiga sun harbi mutum biyu, sun sace babura biu, sannan suka kona motar jami’an tsaro da kuma wata mota, sannan suka yi awon gaba da wata mai shayarwa da danta da wani mutum daya.”

Da yake tabbatar da harin ta cikin wata sanarwa, sakataren yada labaran gwamnan jihar, Bologi Ibrahim, ya bayyana harin a matsayin abin takaici.

Ya ruwaito Gwamna Ibrahim Umar Bago, yana cewa “jami’an tsaron da aka girke a makarantar firamaren Garin Gabas sun yi artabu da wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton sun koro shanun sata, inda a yayin arangamar suka sace mutum uku, jami’an tsaro biyu suka samu rauni.”

Sanarwar ta ce Gwamna Bago ya jajanta wa iyalan da abin ya shafa da kuma  daukacin Masarautar Kagara game da lamarin.