Cristiano Ronaldo ya yi wa abokin hamayyarsa Lionel Messi da Neymar da Kylian Mbappe zarra, a matsayin dan wasan da ya fi kowa kudi a duniya cikin shekarar bana ta 2023.
Fitacciyar mujallar Forbes ta wallafa cewa Ronaldo ya samu kudaden da yawansu ya kai euro miliyan 211 a 2023, sama da abin da takwarorinsa fitattu suka samu.
- Yadda farashin kayayyaki ya yi tashi mafi girma cikin shekaru 20 a Najeriya
- Ma’aikatan Lantarki sun rufe Ofishin KEDCO a Kano
A halin yanzu dai kusan euro miliyan 165 kwatankwacin dala miliyan 200 Ronaldo ke samu a matsayin albashi daga kungiyarsa ta Al Nassr da ke gasar kwallon kafar Saudiya, bayan kulla yarjejeniya da ita a farkon shekarar bana.
Baya ga albashin da yake samu a duk shekara, Cristiano Ronaldo na kuma samun karin kudaden shigar da yawansu ya kai euro miliyan 49, kwatankwacin dala miliyan 60 daga tallace-tallace da sauran yarjeniyoyin da ya kulla da sauran manyan kamfanoni irinsu na Nike da Jacon & Co a duk shekara.
A bangaren Lionel Messi, kididdiga ta nuna cewar kudaden da dan wasan ya samu daga tsohuwar kungiyarsa ta Paris Saint-Germain da kuma Inter Miami da yake taka wa leda a yanzu, ya kai kusan dala miliyan 135 a duk shekara.
‘Yan wasan da ke biye da Messi a matsayi na biyu da na uku su ne Neymar da Kylian Mbappe wadanda ke karbar dala miliyan 112 da kuma dala miliyan 110 a duk shekara.
Dan wasa na biyar mafi kudi a duniya shi ne Karim Benzema da ke samun albashin dala miliyan 106 a duk shekara, sai kuma Erling Haaland a matsayi na 6, wanda kuma shi ne mafi daukar albashi a gasar Firimiyar Ingila, inda yake daukar dala miliyan 58 a shekara.