✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya tsawaita kwantaraginsa a Al Nassr

A ƙarshen watan Yunin da muke ciki ne kwantiraginsa na farko zai ƙare a ƙungiyar da ke Saudiyya.

Cristiano Ronaldo ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwatiraginsa da shekara biyu a ƙungiyar Al Nassr  da ke buga gasar Saudi Pro League.

Wannan dai na nufin kyaftin din na tawagar Portugal zai ci gaba da zama a ƙungiyar har 2027, lokacin da zai kai shekara 42 a duniya.

Al-Nassr ta bai wa Ronaldo kwantiragi mafi tsada a tarihin wasanni, inda ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fam miliyan 24.5 ($33.7m), lamarin da zai ba shi damar samun albashin da zai rika karbar sama da fam miliyan a duk kwana biyu.

Ɗan wasan mai shekara 40 ya je Al Nassr ne a Disamban 2022, bayan raba gari da Manchester United.

A ƙarshen watan Yunin da muke ciki ne kwantiraginsa na farko zai ƙare a ƙungiyar da ke Saudiyya.

Bayan sanya hannun ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar ya ce “An buɗe sabon babin buri da sha’awar ci gaba da kafa tarihi tare” a shafinsa na Instagram.

Duk da cika shekaru 40, Ronaldo ya ci gaba da taka rawar gani, inda a kakar wasan da ta gabata ya zura kwallaye 35 a wasanni 41 da ya buga a duk gasa, lamarin da ya ba shi damar karewa a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar Saudi Pro League a shekaru biyu ke nan a jere.

Ronaldo wanda ke da burin kaiwa kwallaye 1,000, ya zira kwallaye 99 a cikin wasanni 111 da ya buga tun bayan zuwansa Al Nassr, inda ya kawo yanzu ya ci kwallaye 938 jimilla a tarihinsa na tamaula