Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai, UEFA, ta karrama Cristiano Ronaldo da lambar yabo ta gwarzon ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a tarihin Gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Shugaban UEFA, Aleksander Ceferin ne ya miƙa wa Ronaldo kyautar a yayin bikin fitar da jadawalin Gasar Zakarun Turai ta bana da aka a gudanar yau Alhamis a birnin Monaco na Faransa.
Ceferin wanda ya bayyana gasar a matsayin wadda ta fi kowacce fi muhimmanci, ya ce an karrama Ronaldo da kyautar ne saboda babban tarihin da ya kafa a Gasar Zakarun Turai.
Cristiano Ronaldo ya ce sabuwar kyautar da aka ba shi za ta samu muhimmin waje a daykinsa na adana kayan tarihi a birnin Madeira da ke Portugal.
Ronaldo wanda a yanzu yake murza leda a Saudiyya, ya ci jimillar ƙwallo 140 a ƙungiyoyi uku da ya buga wa wasa a Turai da suka haɗa Manchester United, da Real Madrid, da kuma Juventus.
Ɗan ƙwallon na ƙasar Portugal mai shekara 39 ya shafe mafi tsawon rayuwar ƙwallonsa a ƙungiyoyin Sporting CP, da Manchester United, da Real Madrid, da Juventus, kafin ya koma Al-Nassr ta Saudiyya.