✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jadawalin Gasar Zakarun Turai ta bana

Yawan wasannin da za a fafata a sabon tsarin zai ƙaru daga 125 zuwa 189.

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai ta UEFA, ta fitar da jadawalin Gasar Zakarun Turai ta Champions da za a fara amfani da shi a kakar wasa ta bana mai ƙungiyoyi 36.

UEFA ta fitar da jadaalin ne yayin da ta karrama Cristiano Ronaldo da lambar yabo ta gwarzon ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a tarihin Gasar Zakarun Turai.

A Yammacin wannan Alhamis ɗin ce UEFA ta raba jadawalin sabon tsarin gasar wanda Gianluigi Buffon ya halarta a matsayin gwarzon mai tsaron raga a duk duniya kamar yadda Shugaban UEFA, Aleksandr Ceferin ya bayyana.

Real Madrid mai riƙe da Kofin Gasar Zakarun Turai ce za ta fafata da Liverpool da Borussia Dortmund a zagayen farko na gasar da aka sauya wa fasali ta 2024-25.

Kwamitin Zartarwa na UEFA ya yi wa gasar wani muhimmin sauyi na ficewa daga tsarin matakin rukuni da ake yi a baya, inda a yanzu kowace ƙungiya za ta buga wasa takwas — huɗu a gida, huɗu a waje.

A baya matakin rukuni na Gasar Zakarun Turai ya ƙunshi ƙungiyoyi 32, da ake raba wa cikin rukuni takwas, inda kowanne rukuni ke ƙunshe da ƙungiyoyi huɗu.

Sauran wasannin da za su fi zafi a zagayen sun haɗa da wanda PSG za ta kara da ƙungiyoyin Manchester City, Bayern Munich, Atletico Madrid da Arsenal.

A yanzu dai ƙungiyoyi 36 ne za su shiga gasar, mai tsarin lig ɗaya, inda duka ƙungiyoyin za su kasance a teburi ɗaya.

Domin tantance ƙungiyoyin da za su fafata da juna, da farko an rarraba su a cikin tukwane huɗu bisa matsayin kowace ƙungiya.

An yi amfani da wata manhaja da UEFA ta samar domin fitar da ƙungiyoyin da kowacce ƙungiya za ta fafata da su.

Sannan a matakin farko babu ƙungiyar da za ta fafata da abokiyar hamayyarta da suka fito daga ƙasa ɗaya.

Hakan na nufin kowace ƙungiya za ta kara da ƙungiyoyi biyu daga kowace tukunya cikin huɗu.

Yadda tsarin jadawalin manyan kungiyoyin Turai ya kasance:

Real Madrid: Borussia Dortmund (H), Liverpool (A), AC Milan (H), Atalanta (A), Salzburg (H), Lille (A), Stuttgart (H), Brest (A).

Barcelona: Bayern Munich (H), Borussia Dortmund (A), Atalanta (H), Benfica (A), Young Boys (H), Crvena Zvezda (A), Brest (H), Monaco (A).

Bayern Munich: PSG (H), Barcelona (A), Benfica (H), Shakhtar Donetsk (A), Dinamo Zagreb (H), Feyenoord (A), Slovan Bratislava (H), Aston Villa (A).

PSG: Man City (H), Bayern Munich (A), Atletico Madrid (H), Arsenal (A), PSV (H), Salzburg (A), Girona (H), Stuttgart (A).

Yadda tsarin jadawalin kungiyoyin Ingila ya kasance:

Manchester City: Inter Milan (H), PSG (A), Club Brugge (H), Juventus (A), Feyenoord (H), Sporting CP (A), Sparta Praha (H), Slovan Bratislava (A).

Liverpool: Real Madrid (H), RB Leipzig (A), Bayer Leverkusen (H), AC Milan (A), Lille (H), PSV Eindhoven (A), Bologna (H), Girona (A).

Arsenal: PSG (H), Inter (A), Shakhtar (H), Atalanta (A), Dinamo (H), Sporting (A), Monaco (H), Girona (A).

Celtic: RB Leipzig (H), Borussia Dortmund (A), Club Brugge (H), Atalanta (A), Young Boys (H), Dinamo (A), Slovan Bratislava (H), Aston Villa (A).

Aston Villa: Bayern Munich (H), RB Leipzig (A), Juventus (H), Club Brugge (A), Celtic (H), Young Boys (A), Bologna (H), Monaco (A).

Me zai faru idan aka kammala zagayen farko?

Idan aka kammala wasannin zagayen farko (kowace ƙungiya ta kara da ƙungiyoyin da aka haɗa ta da su), ƙungiyoyin za su kasance a teburi ɗaya wato daga na ɗaya zuwa na 36.

Daga nan ne kuma sai ƙungiyoyi takwas na saman teburi su tsallaka kai-tsaye zuwa zagayen ‘yan 16, yayin da daga kan ƙungiya ta tara zuwa 24 za su yi wasan neman gurbi (gida da waje), don kaiwa zagayen ‘yan 16.

Su kuwa waɗanda suka ƙare a matsayi na 25 zuwa 36, an fitar da su daga gasar kenan, kuma ba za su samu damar shiga gasar Europa League ba, kamar yadda ake yi a baya.

Daga kan matakin zagayen ’yan 16 kuma sai a ci gaba da yadda aka saba gudanar da ita a baya — wato a kai matakin kwata-final, da matakin dab da na ƙarshe, har zuwa wasan ƙarshe, wanda za a yi a birnin Munich na ƙasar Jamus.

Yawan wasannin da za a fafata a sabon tsarin zai ƙaru daga 125 zuwa 189.

Kowace ƙungiya za ta yi wasa takwas mafi ƙaranci maimakon shida da ƙungiyoyin da ake fitarwa daga gasar tun a rukuni ke samun damar yi a baya.

Za a gudanar da wasan zagayen farko har zuwa ƙarshen watan Janairu, maimakon a baya da yake ƙarewa kafin bikin Kirsimeti.

Kungiyoyin da za su fafata a gasar

Tukunyar farko: Real Madrid (Spa), Man City (Eng), Bayern Munich (Ger), Paris St-Germain (Fra), Liverpool (Eng), Inter Milan (Ita), Dortmund (Ger), Leipzig (Ger), Barcelona (Spa)

Tukunya ta biyu: Bayer Leverkusen (Ger), Atletico Madrid (Spa), Atalanta (Ita), Juventus (Ita), Benfica (Por), Arsenal (Eng), Club Brugge (Bel), Shakhtar Donetsk (Ukr), AC Milan (Ita)

Tukunya ta uku: Feyenoord (Ned), Sporting Lisbon (Por), PSV Eindhoven (Ned), Dinamo Zagreb (Cro), Salzburg (Aus), Lille (Fra), Red Star Belgrade (Ser), Young Boys (Sui), Celtic (Sco)

Tukunya ta huɗu: Slovan Bratislava (Ska), Monaco (Fra), Sparta Prague (Cze), Aston Villa (Eng), Bologna (Ita), Girona (Spa), Stuttgart (Ger), Sturm Graz (Aus), Brest (Fra).