✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa da jaririyarta sun mutu a hatsarin kwalekwale a Adamawa

Har yanzu ba a gano gawarwakin uwar sa jaririyar ba.

Akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin ruwa a kauyen Gamadio da ke Karamar Hukumar Numan a Jihar Adamawa.

Rahotanni sun bayyana cewar wata mata ce da jaririyarta suka rasu a jirgin ruwan da ke dauke da mutane biyar da ya kife ana tsaka da tafiya.

Har yanzu dai ba a gano gawarwakin mutanen biyu ba, amma Shugaban Karamar Hukumar Numan, Christopher Sofore, ya ce an ceto sauran mutane ukun.

Sofore ya yi magana ne a lokacin da tawagar jihar karkashin jagorancin mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa George Farauta, ta ziyarci Numan.

Farfesa Farauta ya kalubalanci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da samar da rigunan kwalekwale don rage asarar rayuka.

Ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da kai rahoton faruwar irin wannan lamari a kan lokaci ga hukumomin da abin ya shafa.