Akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin ruwa a kauyen Gamadio da ke Karamar Hukumar Numan a Jihar Adamawa.
Rahotanni sun bayyana cewar wata mata ce da jaririyarta suka rasu a jirgin ruwan da ke dauke da mutane biyar da ya kife ana tsaka da tafiya.
- Za a farfado da harkar wasanni don magance shaye-shayen matasa a Gombe
- Dalilin Da Maza Ke Haura Shekar 40 Babu Auren Fari
Har yanzu dai ba a gano gawarwakin mutanen biyu ba, amma Shugaban Karamar Hukumar Numan, Christopher Sofore, ya ce an ceto sauran mutane ukun.
Sofore ya yi magana ne a lokacin da tawagar jihar karkashin jagorancin mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa George Farauta, ta ziyarci Numan.
Farfesa Farauta ya kalubalanci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da samar da rigunan kwalekwale don rage asarar rayuka.
Ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da kai rahoton faruwar irin wannan lamari a kan lokaci ga hukumomin da abin ya shafa.