Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba wa takwarorinsa na gwamnonin Jihohin Borno, Bauchi, Adamawa, Gombe da Taraba a bisa ga samun damar da suka yi na halartar taron ƙungiyarsu ta Arewa maso Gabas (NEGF) karo na 11 a garin Damaturu.
Ya yi wannan yabo ne a ranar Alhamis a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Damaturu yayin jawabinsa na maraba yadda ya bayyana fatansa cewa, taron zai samar da sabbin dabarun yaƙi da rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki.
- Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas
- Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara
Buni ya bayyana wannan ƙungiyar a matsayin wani muhimmin dandali na haɗin gwiwa da daidaita manufofi, musamman yadda yankin ke fama da sabbin hare-hare daga ƙungiyar Boko Haram da kuma amfani da fasahar zamani wajen kai hare-hare.
“Wannan taron ya zo kan lokaci. Dole ne mu yi aiki da sauri don ƙarfafa nasarorin da muka samu wajen gina zaman lafiya da farfaɗo da tattalin arziki,” in ji shi.
Ya yi kira da a raba ƙudurori daga taron da hukumomin tsaro na tarayya domin bunƙasa haɗin kai da hanyoyin mayar da martani cikin gaggawa.
Gwamna Buni ya kuma nuna jin daɗinsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayansa da jagoranci, sannan ya mika godiyarsa ga rundunonin sojan ƙasar, rundunar hadin gwiwa ta farar hula da masu aikin sa kai bisa sadaukarwar da suka yi.
A kan farfaɗo da tattalin arziki, ya yi kira wajen neman saka hannun jari a harkar noma, samar da ayyukan yi da kuma shirye-shiryen rayuwa mai ɗorewa.
“Dole ne mu sanya aikin noma ya zama abin sha’awa, mai araha, kuma mai riba don amfani da albarkatun ƙasa da na ɗan Adam,” in ji shi.
Ana sa ran taron zai fitar da ƙudurori da nufin ƙarfafa ayyukan tsaro na haɗin gwiwa, da daidaita ayyukan jin ƙai da inganta kasuwanci da zuba jari a yankin.
Yayin da yankin ke ci gaba da bin hanyoyin farfaɗowa, hakan ya sake tabbatar da abu guda: hanyar samar da zaman lafiya da walwala wadda ta ta’allaka ne a cikin haɗin kai da hangen nesa da aiki tuƙuru.
Da yake jawabin maraba ga gwamnonin na Arewa maso Gabas wajen wannan taron shugaban Ƙungiyar gwamnnonin Arewa maso Gabas Farfesa Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya bayyana irin ƙalubalen da wannan yanki ke fuskanta dangane da harkokin tsaro da kuma talauci, yadda ya nemi al’ummomin yankin da su yi ƙoƙari wajen ganin an samu canji.
Ya kara da cewa, akwai buƙatar da haɗa kai don ganin an samu nasarar wajen shawo kan wannan matsala ta dawo da taɓarɓarewar harkokin tsaro a wannan yanki wadda kuwa babbar matsala ce.