Wani dattijo mai suna Alhaji Muftau Mohammed da ke unguwar Gbeganu a Minna, babban birnin jihar Neja, ya faɗi ya mutu a ofishin ‘yan sanda na Morris.
Bayanai sun ce ajali ya katse wa mutumin hanzari ne yayin da ya je belin ’ya’yansa biyu waɗanda rahotanni suka ce ‘yan sandan sun kama su.
’Ya’yan marigayin — Mubarak da Yusuf — sun shaida wa Aminiya cewa, ‘yan sanda sun kama su ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Laraba lokacin da suke barci a a harabar da ke gaban ƙofar gidansu saboda yanayin zafi.
A cewar Yusuf, “Muna kwance a ƙofar gidanmu da misalin ƙarfe 11:23 na dare, sai ga wasu motocin ‘yan sanda guda uku da ke sintiri suka wuce mu, suka shiga Unguwar Gbeganu.
“Bayan ’yan sa’o’i kaɗan, sai muka ga suna dawowa kuma muka tashi.
“Nan da nan sai ga motar da ke tsakiya ta taho a gabanmu, suka tambayi me muke yi a waje.
“Sai muka sanar da su cewa a nan ne muke kwana saboda zafi.
“Ana tsakar haka sai ɗaya daga cikin jami’an ya umarci abokan aikinsa su saka mu a cikin motar su kai mu ofishin su.
“Lokacin da muka isa ofishin ‘yan sandan Morris, sun ƙwace wayoyinmu suka saka mu a cikin sel.
“Bayan kamar minti 20, ina cikin sel sai na ji muryar mahaifina a waje.
“Daga baya na ji shi yana kururuwa, yana neman ruwa da ‘yan daƙiƙa kaɗan, ban sake jin komai ba.
“A lokacin ne na tambayi ɗaya daga cikin jami’an abin da ke faruwa a waje. Amma ɗaya daga cikin jami’an ya ce, abokin aikin nasa kada ya gaya mana komai. Daga baya ban sake jin muryar mahaifinmu ba sai dai aka ce mana ya rasu.”
Shi ma da yake jawabi, maƙwabcin marigayin Mista Dauda Jimo wanda ya kai shi a kan babur ɗinsa zuwa ofishin ‘yan sanda a wannan daren, ya ce Alhaji Muftau Mohammed yana da hawan jini kuma duk lokacin da ya shiga ɓacin rai, yakan kamu da ciwon kai mai tsanani.
“A gabana ne ‘yan sanda suka kama ’ya’yansa maza, lamarin da ya sanya ya farka daga barci.
“Saboda hayaniyar ’ya’yansa mata da na maƙwabta ne suka tashe shi da ɓacin rai. Don haka da suka ce masa ‘yan sanda sun tafi da Mubarak da Yusuf, sai ya kira ni na kawo babur na kai shi ofishin ‘yan sanda.
“Mun isa ofishin ‘yan sanda da misalin ƙarfe 12:33 na tsakar dare.”