✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Adam Zango ya girgiza teburin Kannywood

Adam A. Zango ya ya jero wasu maganganu na fallasa da suka shafi iyalansa da abokan harkarsa.

A farkon wannan mako ne fitaccen jarumin nan na Kannywood Adam A. Zango ya girgiza teburin Masana’antar Finafinan Hausa ta Kannywood, inda ya jero wasu maganganu na fallasa da suka shafi iyalansa da abokan harkarsa.

Adam A. Zango wanda tun farko sai da ya yi kashedi kan abin da zan fada a faifan bidiyon da ya saki ya yi zargin cewa.

“Idan kana son cincirindon mayaudara, mahassada, betrayers masu kyashi ka shigo Kannywwod amma fa ba duka ba.

“A yau idan na daina fim na daina waƙa kun yi nasara a kaina amma idan har zan fita cikin masana’antar ku ji farin ciki ku ji dadi amma ni zan fi samun farin ciki da jin dadi na fita a cikinku zan zauna da iyalaina lafiya, zan zauna ni kadai da dangina lafiya, online din ma ba lallai ku gan ni ba, saboda ni wannan midiya da nake yi dole ce ta sani yi, ni ba ma’abucin midiya ba ne.”

Ba a nan Adam Zango ya tsaya ba, ya ƙara da cewa: “Idan na gaya maku adadin mutanen da na bai wa gudunmawa a Masana’antan Kannywood lissafasu ma zan zan yi yanzu za ku sha mamaki duk wanda na kira sunansa billahillazi la’ilaha illalhuwa na ba shi kashi talatin ko hamsin.

“Amma ba ku taba jin sunansa a bakina ba, asali ma in sun budi baki sun fadi wanda ya taimake su sai dai su kira wani ba maganar Adamu Zango ba, saboda ni wulaƙantacce ne ban san me nake yi ba a sama da shekara 20 ana harkar nan da ni.”

Ya ce abubuwan da ke zuciyarsa a sama da shekara 10 sun isa su fasa zuciyar, inda ya ce zama mai suna masifa ce ba alheri ba ne, rayuwa ce ta ƙarya da ke tattare da baƙin ciki.

Ya ce a Masana’antar Kannywood mutumin da ke ƙoƙarin kare mutuncinsa ’yan Kannywood kuma sai ƙu riƙa ƙoƙarin tona masa asiri da zubar da mutuncinsa.

“Idan na koma maku daga baya billahillazi da kudina da gumina in je gala, in dauki fim in saki, in tafi biki, in yi talla, in tara kudina in dauki kudina in sayi mota in bai wa mutum, amma kun taɓa jin wani ya kare ni?

“Kafin kowa ya fara ba da mota a Kannywood ni na fara, na ba da mota sun fi bakwai, ba a wajen wani na karɓa ba, ba wani na roƙa ba, na saya na bayar amma babu wanda zai iya fitowa ya kalli duniya ya kare wa Adamu mutuncinsa a kan abin da aka sani ba halin Adamu ba ne, sai mutum na da matsala, matata ta haihu, zan kama gida ba ni da ciko.

“Zan yi aure ba ni da lafiya mamana ba ta da lafiya ba ni da abinci sannan a same ka a daki a roƙe ka ka dauka ka bayar a fito duniya ana zaginka sai su yi shiru idan na kare Adamu Zango jarumi wane ba zai yi mu’amala da ni ba, Furodusa wane, darakta wane ba za su yi mu’amala da ni ba. Domin haka zan rufe alherinsa kawai in yi shiru.

“Falalu Ɗorayi, Sadik Mafiya, Tahir I. Tahir, Abubakar Sani, Kabiru, Rabi’u, Umar Big Show duk wadannan mutane na ba su mota da kudina, akwai lokacin da na yi biki na kyautar da babura da kudina ba amma yau wa gari ya waya, butulci!

“Mutanen da na bai wa gudunmawa ga su nan birjik amma a shekara goma babu mutum daya da ya taɓa fitowa, ya fadi alherin Adamu ko ya kare shi, duk wanda na kira yanzu ka gaya masa idan ya manta, ni ban manta ba, Fati Nijar, Nazifi Asnanic, Zainab Raga, Zainab Indomie, Umar Bishir, Ali Jita, Ado Gwanja,Umar M. Sharif, Sadik Sani Sadik, Isa Faroskhan, Usaini Danko, Jarumai ko irin su Fati sai na aure Zango, Malika, Samira ’yar Ƙarama, Amina soyayya da shakuwa, wadannan fa suna da rai, amma haka suka yi shiru kuma haka suke sa ran zan ci gaba da kallonsu a mutanena masoyana, ba zai taɓa yiwuwa ba!”

Adam Zango ya ce duk abin da ke faruwa a rayuwarsa laifin ’yan Kannywood ne saboda ba su yi masa adalci, ladabi da biyayya, kyautatawa, kare mutuncinsa ba su taya shi ba.

“Ba ni da mutunci, duk wanda ya tashi zai fadi abin da ya ga dama a kaina, abin da kuke gani a soshiyal midiya kadan ne a kan abin da ake yi min a Kannywood domin a ɓata ne ta yadda za ku sha mamaki idan na bude baki na fada muku,” in ji shi.

Sai ya ƙara da cewa: “Nan matar da na aure ta ta fito ta fadi ƙarya da gaskiya a kaina kuka yarda. Na fito na yi magana kuka yi ca ba ka da kaza ka daina sirrinka ne wane sirri?

“Wani dan jaridar soshiyal midiya yake kiran matata da ’yar uwanta suna ba shi bayanin sirrin gidana bayan mun rabu.

“Duk abin da tsohuwar matata take yi ina ji, ku ba kwa ji, ina gani ku ba kwa gani, daga ƙafa kawai na yi na rabu da ita, albarkacin ’yata amma ba don haka ba na rantse da Azza Wa Jallah, abu daya idan na fito na fada a kanta rayuwarta ta ƙare wallahi…idan na fito na yi magana sai kun ce min ashe kai sahabi ne, ita ta san haka tana da damar ta fito ta yi magana.”

Martanin ’yan Kannywwod

Wasu daga cikin ’yan masana’antar sun magantu kan wannan girgiza teburin da Adam Zango ya yi: Ali Jita ya ce, “A gaskiya mun yi kuskure, abin da muka yi wa Adamu domin ya taimake mu. Kuma bai kamata a ce don mun samu daukaka mu manta da shi ba.”

Ya ce za su yi ƙoƙari su ga abin da za su iya yi domin gano abin da ke damun Jarumi Zango tare da taimaka masa.

“Allah Ya sawwake mutum ya yi mana rana sannan mu yi masa dare. Ba za mu taɓa zama masu butulci ba. A matsayina na Shugaban ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya ina magana a madadin ’ya’yan ƙungiyar da suka hada da Ado Gwanja da Nazifi Asnanic.

Idan Allah Ya yarda za mu zauna da shi mu fuskanci matsalarsa tare da daukar matakin magance ta,” in ji shi.

Jarumin barkwancin Mustapha Naburuska ya ce “Duk maganganun da Adamu ya yi gaskiya ya fadi domin da ciwon ƙwarai da gaske ka ga mutumin da ka taimaka a rayuwa ya yi watsi da kai.

“Yana ji yana gani ana ci maka mutunci ba zai iya yi kare ka ba. Za ki ga duk lokacin da aka yi masa wani abu na wulaƙanci maimakon a fito a kare shi sai ki ga an yi banza da shi. Na tabbata idan aka fito aka kare shi zai ji dadi domin zai san cewa ana tare da shi.

“Amma daga inda aka taɓa muhibbarka ba ka samu wasu sun zo sun kare ka ba to fa akwai damuwa.”

Naburuska ya ƙara da cewa, “Mu shaida ne mun san irin taimakon da ya yi wa mutane masu yawa a wannan masanaanta tamu.

“Ni kaina na ci gajiyar taimakonsa domin ya taimake ni dari bisa dari, kai dubu bisa dubu. A wurin Adamu idan ban zama na uku ba, to zan zama na hudu. Ba ni da bakin godiya a kan irin taimakon da ya yi min.

“Har yanzu muna zaman amana da mutunta juna. Fadin abin da ke ransa aƙalla samun sauƙi ne a zuciyarsa, domin a cikin mutum 10, za a iya samun hudu su fahimci inda ya sa gaba.

“A gaskiya Adam Zango mutum ne mai ƙima da daraja wanda yake girmana dan Adam fiye da zaton mutane. Ba za ka san ko shi wane ne ba sai ka kusance shi.”

“Ita kuwa mawaƙiya Fati Nijar cewa ta yi: “Ina Neman afuwar dan uwana abokin aikina. Na san kai mutumin kirki ne mai taimakon mutane domin ni kaina ka taimaka min a lokacin da nake buƙatar taimako.

“Ina iya tunawa a lokacin da muke Kamfanin Sulfur kana koya min waƙa. Babu shakka an yi zaman mutunci da zumunci. Ina neman afuwarka bisa abin da kake ganin na yi maka na ba daidai ba.

“A gaskiya hankalinka bai kai kan batun ba ka kariya ba. Idan Allah Ya yarda idan ka dawo Nijeriya har gida zan zo in ba ka haƙuri.”

Sai ta shawarci jarumin ya riƙa kau da kai daga maganganun ɓata suna da ake yi masa, “Don Allah ina roƙonka ka riƙa kau da kai daga irin wadannan maganganu da ake yi a kanka. Idan zai yiwu ma daga wannan kada ka sake magana a kan hakan a soshiyal midiya,” in ji ta.

Jarumin barkwanci da aka fi sani da Abale shawartar abokan sana’arsa ya yi cewa zai yi kyau su zauna da Jarumi Zango don jin damuwarsa.

Da Aminiya ta leƙa shafukan sadarwar wasu jaruman ta tsakuro wani au daga abin da suka ce: @Baballehayatu ya ce: “Haba Adamu, me ya yi zafi haka?

“Ina ga kamar mun yi wannan magana, idan akwai wani abu sai ka kira a waya kawai mu nemi mafita tare. komai ya yi zafi maganinsa Allah… ba abin da ya fi ƙarfin Allah… haba Adamu ina imaninka? Ina tunaninka? Ina maganganun da muka zauna muka yi da kai da ’yan uwa da yawanmu? Ya kamata mu sake zama.

@Ayshatulhumairah cewa ta yi: “Komai ya yi zafi maganinsa Allah. Duk abin da ya fi ƙarfinka ba zai fi ƙarfin Ubangijinka ba. Allah Ta’ala Ya kawo maka mafita a cikin rayuwarka Ya yaye maka duk damuwarka.”

@safzorofficial ya ce: “Allah Ya mana mai kyau Allah Shi ne Masanin komai amma daukaka da dadi da wuya haka ka ce a wata waƙarka. Don haka ina mai ƙara ba ka haƙuri a bar wa Allah lamarin zai yaye komai don Manzon Allah (SAW). Simba Always Simba”

@sadisidi_sharifai kuwa ya ce: “Ka mance da zancen nan babu wanda ya isa ya hana ka sai ikon Allah.

@Ummabamalli ta ce: “Babban Haidar kada ka bari ƙuncin rayuwa ya yi tasiri a kanka don girman Allah, ka yi haƙuri ka kwantar da hankalinka ko don yaranka…ka sauka a social media na dan wani lokaci komai zai faru ka ce kada wanda ya fada maka in ba abin farin ciki zai fada maka ba. Ka tafi inda ka san hankalinka zai kwanta sannan ka sami doctor (likita) wanda zai dinga duba lafiyarka, in sha Allahu komai zai wuce ka yi haƙuri kowa da irin tasa irin jarrabawar …”

@sultan_abdurrazaƙ_doraya ya ce: “Ba wai iya fim da waƙa ba ne kawai, komai kake yi a wannan al’umma tamu, matuƙar ka samu daukaka a cikinsa, kuma ka ce ba za ka toshe kunnenka ka kawar da kanka ba, to, fa mutane ba za su taɓa barinka ka zauna lafiya ba…”