Shugaban Hukumar Fina-finai ta Kasa, kuma tauraro a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, ya kai wa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ziyarar ban-girma.
Ana iya cewa, zuwan Ali Nuhu Fadar Sarkin Kano tare da wasu fittattun ’yan Kannywood, ita ce ziyarsa ta farko ga sarakuna a fadin Najeriya tun bayan nada shi a mukamin.
Bayan ziyarar ce, Ali Nuhu ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Godiya da jinjina ga Mai Martaba Sarkin Kano @hrh_aminu_ado_bayero CRR CNOL JP da irin adduo’i da shawarwari da aka ba mu.
“Allah Ya bamu ikon yin biyayya a matsayin mu na ’ya’ya, Ya kuma ja da ran sarki, Allah Ya rika da hannayenka, bijahi rasulillah sallalahu alaihi wa sallam.
- AFCON 2023: Babu tabbacin Osimhen zai buga a wasan Najeriya da Afirka ta Kudu
- An kama mata ’yan bindiga a Abuja
- Saurayi ya fille kan budurwarsa a Bayelsa
“Allah Ya sa wannan mukami ya zama alheri, Ya kuma kare mu daga duk wani sharri da ke tare da shi,” in ji shugaban hukumar fina-finan.
Kano dai ita ce cibiyar Kannywood, uwan masana’antar fina-finan Hausa a Arewacin Najeriya da ma ketare.
Masana’antar wadda daga cikinta Ali Nuhu ya fito, ya kuma samu daukaka na fatan shugabancinsa a hukumar zai ba ta damar samun ci gaba da kuma karin shiga a wajen gwamnati ta yadda za a rika damawa da ita yadda ya kamata.
Masana’antar Kannywood dai ta taka muhimmiyar rawa ta hannun mawaka da sauran jarumanta a lokacin yakin neman zabe, inda kuma suke fata ba za su tura mota ta tafi ta bar su da kura ba.