✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saurayi ya fille kan budurwarsa a Bayelsa

An wayi gari saurayin ya sare kan budurwar da suka jima tare.

An shiga rudani a Karamar Hukumar Sagbama a Jihar Bayelsa, yayin da wani saurayi ya fille kan budurwarsa.

Ko da yake babu cikakken bayani game da yadda lamarin ya faru, amma ta gano budurwar mai suna Maxuel Ebibraladei da saurayin nata, sun haifi yaro a waje.

Ana zargin saurayin ya kashe ta ne da misalin karfe 3 na daren ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewar mazauna yankin sun cafke shi tare da mika shi ga ’yan sanda kafin ya tsere.

’Yan sanda sun ajiye gawar marigayiyar a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa.

Tuni aka mika saurayin ga sashen ‘yan sanda masu binciken manyan laifuka na (CID).

“Ba mu san abin da ya faru a tsakanin masoyan biyu da zai sa ya sare kan budurwarsa kuma uwar ɗansa ba.

“Su biyun sun kasance cikin zaman lafiya. Mun kasa tantance abin da ya faru,” cewar wani mazaunin yankin.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Musa Muhammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce rundunar za ta fitar da sanarwa a game da lamarin.