✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 6 sun rasu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Ebonyi

Kwamandan ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun ganganci.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Ebonyi ta tabbatar da rasuwar mutum shida a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Afikpo zuwa Abakaliki.

Kwamandan hukumar a jihar, Igwe Nnabuife, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abakaliki cewa hatsarin ya rutsa da mutum 17.

Nnabuife, ya ce mutum shida sun mutu, yayin da 11 suka samu munanan raunuka.

A cewarsa, hatsarin ya rutsa da motoci uku da kuma wasu manyan motoci biyu.

“Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 11:50 na safe a yankin Onuwedu, da ke Karamar Hukumar Ezza ta Kudu a Ebonyi.

“Hatsarin ya faru ne, sakamakon gudun wuce kima.

“An kai gawar wadanda suka mutu Asibitin Koyarwa na Tarayya na Alex Ekwueme da ke Abakaliki.

“Wadanda suka jikkata likitoci na ba su kulawa.

“Muna bai wa direbobi shawara su kasance masu hakuri yayin tuki. Su kasance masu bin dokokin hanya, hakan na da matukar muhimmanci. A guji tukin ganganci don ceto rayuka,” in ji Nnabuife.