✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram Ta Kashe Magina Ta Sace Mafarauta A Yobe

Wasu mahara da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe wasu masu aikin gini biyu tare da yin garkuwa da mafarauta uku a gidan…

Wasu mahara da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe wasu masu aikin gini biyu tare da yin garkuwa da mafarauta uku a gidan hakimin garin Kukaretra da ke Karamar Hukumar Damaturu a Jihar Yobe.

Basaraken ya ce ’yan ta’addan da suka kai hari da misalin karfe 3 na asubahin ranar Lahadin sun shafe awa guda suna harbe-harbe, suka kona gidan nasa na motarsa, sannan suka kashe wasu daga cikin bakin nasa, suka sace wasu, a gidan da kan titin zuwa Maiduguri.

Hakimin garin, Alhaji Lawan Babagana, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa ’yan ta’addan “Da misalin karfe 3 na asubahin ranar Lahadi suka kawo farmaki wannan gari namu suka rika harbe-harbe, suka banka wa gidana wuta, suka kona motata kirar Peugeot 504, sannan suka lalata gida daya a garin.

“Mutane biyar ne a gidana, wadanda masaukin bakina ne; biyu daga cikinsu ma’aikatan gine-gine ne da Hukumar Raya Arewa maso Gabas ta kawo daga Adamawa, domin gina Kasuwar Kukareta.

“Kamar yadda kuka sani a matsayina na sarkin gargajiya, nakan karbi bakuncin mutanen da ke zuwa yankina; Wadannan yara  mayakan Boko Haram ne, sun fito da wadannan ma’aikatan daga gidana, suka harbe su nan take.

“Akwai mafarauta guda uku, wadanda nake karbar bakunci a gidana, inda wadannan ’yan ta’adda suka daure, suka yi garkuwa da su a cikin motar ’yan banga da aka ajiye a gidana,” Inji shi.

“’Yan sanda sun kwashe ragowar ma’aikatan ginin tare da kai su asibitin kwararru da ke Damaturu don duba lafiyarsu,” in ji shi.