✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2023: Babu tabbacin Osimhen zai buga a wasan Najeriya da Afirka ta Kudu

’Yan Najeriya na neman Super Eagles su huce musu haushinsu bayan mawakiyar Afirka ta doke mawakan Najeriya hudu wajen lashe kambin mawakan duniya na Grammy

Alamu na nuna ba lallai ba ne dan wasan Najeriya Victor Osimhen ya buga a Wasan Kusa da na Karshe tsakaninsu da Afirka ta Kudu a Gasar Kofin Afirka (AFCON 2023).

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ken neman Super Eagles, musamman Osimhen da Lookman su huce musu haushinsu bayan mawakiyar Afirka ta Kudu Tyla ta doke mawakan Najeriya hudu wajen lashe kambin mawakan duniya na Grammy a ranar Lahadi.

Da misalin karfe 6 yamma ranar Laraba Super Eagles za ta barge gumi da Afirka ta Kudu a gasar da ke gudana a kasar Kwaddibuwa.

Idan Super Eagles Afirka ta yi rashin nasara a wasan, to Afirka ta Kudu ta yi wa Najeriya duka biyu ke nan a cikin kwana uku, a fannin waka da kuma kwallon kafa.

A ranar Litinin Super Eagles ta sanar cewa Osimhen na fama da rashin lafiya kuma sauran ’yan wasan sun tafi birnin Bouaké, inda za su fafata da Bafana-Bafana na Afirka ta Kudu.

Jami’in yada labaran tawagar ’yan wasan Najeriya, Babafemi Raji, ya ce “sauran ’yan wasan sun bar Osimhen a birnin Abidjan inda likitoci ke lura da shi; Amma idan ya samu sauki, gobe (Talata) to zai same su kafin karfe 5 na yamma.”

Masoya kwallon kafa a Najeriya dai na son ganin Gwarzon Dan Wasan Afirkan a wasan, ganin yadda ya nuna hazaka a sauran wasannin gasar.

Wasu ’yan kasar na son ganin yadda shi da takwarorinsa sun casa Afirka ta Kudu a wasan domin huce haushinsu kan rashin lashe kyauta da mawakan kasar suka yi a bikin rabon kyauttukan Grammy Awards da aka gudanar ranar Lahadi.

Fitattun mawakan Najeriya hudu ne —  Burna Boy, Ayra Starr, Davido, Asake and Olamide — aka gabatar da sunayensu domin samun kyauta a bikin wanda shi ne karo na 66, amma mawakiyar Afirka ta Kudu, Tyla ta doke su, wanda bai yi wa ’yan Najeriya dadi ba.

Mawakiyar Najeriya Teni na daga cikin wadanda suka roki Super Eagles, musamman Osimhen da Lookman da su huce musu haushinsu a kan Afirka ta Kudu kan kyautar Grammy din da ’yan kasar suka rasa.

“Osimhen da Lookman ku muke jira mu ga me za ku yi musu. So muke ku casa mana su, har sai sun yi rawar Amapiano bayan kun gama da su a AFCON,” in ji mawakiyar a wani bidiyonta na Instagram kan batun na Grammy.