Gwamnatin Amurka ta sanar da janye tallafin da take bai wa Afirka ta Kudu yayin da alaƙa tsakanin ƙasashen biyu ta lalace a dalilin dokar karɓe gonakin fararen fata da Shugaba Cyril Ramaphosa ya amince da ita.
Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta katse duk wani tallafin da take ba wa Afirka ta Kudu ciki har da na kuɗi a wani mataki na nuna adawa da dokar kwace filayen noma da Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ya rattabawa hannu.
- Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari
- Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2
Shugaba Trump ya ce Amurka ba za ta taimaka wa gwamnatin Pretoria ba, duba da yadda take ci gaba da take haƙƙin ɗan Adam, da kuma yi wa siyasar Amurka ta ƙetare karan tsaye, inda ya soki zargin Isra’ila da aikata laififukan yaƙin da Afirka ta Kudun ta yi a baya, da ma hulɗarta da Iran a wani ƙudirin da ya sakawa hannu a ranar Juma’a.
Sai dai tun a gabanin matakin na shugaban Trump ya soma aiki, a wani jawabinsa, Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudun ya ce kasarsa ba za ta kawar da ido ga duk wata barazana ba.
Tun farkon wannan wata na Fabrairu ne Donald Trump ya ce zai yanke duk wasu kuɗaɗe da Amurka ke bai wa Afirka ta Kudu har sai an kammala cikakken bincike kan matakin gwamnatin ƙasar na ƙwace filaye mallakar fararen fata ba bisa ƙa’ida ba.
Barazanar na zuwa ne yayin da a ƙarshen watan Janairun da ya gabata Shugaba Ramaphosa ya ƙaddamar da dokar da ta bai wa gwamnati damar ƙwace wasu filaye galibi mallakin fararen fata ba tare da biyan diyya ba a wani mataki na samar da daidaito da kuma adalci ga ’yan kasar.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana matakin a matsayin wani yunƙuri na gyaran kura-kurai na rashin daidaito da ƙasar ta gada daga Turawan mulkin mallakar na Birtaniya.
Sai dai wannan mataki ya gamu da suka daga masu ra’ayin mazan jiya ciki har da attajirin nan Elon Musk ɗan asalin Afrika ta Kudu wanda ke da kusanci da shugaba Donald Trump.